Kawo yanzu dai babu wani dan wasa da yake nuna bajinta daga nahiyar Afirka a gasar Firimiya kamar dan wasa Muhammad Salah na kasar Masar wanda yake buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Liverpool domin kusan duk mako sai ya nuna bajinta. Dan wasan gaban na Liverpool ya zura kwallo biyu a wasan da kungiyar ta lallasa Tottenham da ci shida da uku kuma da wannan nasarar ce Salah ya haura dan wasan gaban Manchester City a fafutikar neman zama wanda zai fi zura kwallo a kakar bana.
Bayan zura kwallo 15 a kakar ta bana, Salah ne kuma ke kan gaba wurin taimakawa a zura kwallo, inda bayan wasan na ranar Lahadi, yanzu ya taimaka an zura kwallo 11 ke nan a wasannin da ya bugawa kungiyar a kakar bana.
Dan wasan na Masar yanzu ya kama hanyar maimaita nasarar da ya samu a shekarar 2022, inda ya zama wanda ya fi zura kwallo, sannan ya fi taimakawa a zura kwallo kuma duk da cewa ana ta kwan-gaba-kwan-baya a game da makomar dan wasan – kwantiraginsa zai kare a bana – har yanzu yana ci gaba da nuna bajinta.
Amma yaya za a kwatanta dan wasan mai shekara 32 da sauran zakarun ‘yan wasan da suka buga wasa a gasar ta Premier League ta Ingila?
Makon kafa tarihi
Salah ya fara kakar bana da kafar dama, inda ya zura kwallo 12 a wasa 12 da suka gabata yanzu ya zura kwallo 18, sannan ya taimaka an zura 15, kenan yana da hannu a kwallaye 33, hudu ke nan a gaba da duk wani dan wasa a manyan gasannin Turai.
A wasan Liverpool da Tottenham ya kafa tarihi uku.
Ya zama dan wasa na farko da ya haura sa hannu a zura kwallo, wato zura kwallo da taimakawa a zura sama da goma kafin Kirsimeti.
Na farko da ya taimaka a zura kwallo sama da 10 a kaka hudu a jere. Wannan ce kaka ta shida da Salah ya samu wannan nasarar, inda ya doke tsohon dan wasan Manchester United Wayne Rooney.
Yanzu Salah zai so ya kafa wani tarihin a wannan kakar, inda yanzu ya mayar da hankalinsa kan lashe takalmin zinare na wanda ya fi zura kwallaye a kaka hudu- nasarar da tsohon dan wasan Arsenal Thierry Henry ya taba yi a baya.
Salah ya zura kwallo 18 a duk kakar da ya buga a Liberpool kuma saura kwallo biyar ya zama dan wasa na biyar da ya taba zura kwallo 20 a kaka biyar, sannan dan wasan gaban na Liberpool yanzu yana fafatawa ne da Haaland domin lashe takalmin zinare.
Dan wasan na Norway ya zura kwallo 27 a kakar bara, sannan ya zura kwallo 36 a kaka biyu da ta gabata, inda ya zama dan wasa na farko tun bayan Harry Kane na Tottenham da ya lashe kambun wanda ya fi zura kwallo a kaka biyu a jere.
Shi ma dai Haaland yana so ya lashe kambun a bana, inda yanzu haka shi ma ya zura kwallo 10, amma halin da kungiyar ta Manchester City karkashin jagorancin Pep Guardiola ya sa ana ganin abu ne mai wahala ya lashe gasar.
Yanzu dai babu shakka Salah na cikin gwarazan ‘yan wasan Liberpool, inda ya lashe duk wani kofi da ake bukata a kungiyar kuma shi ne na hudu a cikin wadanda suka fi zura kwallaye a kungiyar, inda yake da kwallo 229 a wasanni 373, kuma yake bukatar kwallo 12 domin kamo Gordon Hodgson.
Roger Hunt na da kwallo 285, Ian Rush na da 346, wadanda sun masa nisa, amma idan zai iya ci gaba da zura kwallo kamar yadda yake yi a yanzu, zai bukaci wasanni 190 kafin ya zarce su, wanda abu ne mai wahala sosai.
A bangaren gwarazan gasar Premier League, yanzu haka Salah na cikin gwanayen ‘yan wasan gasar, inda yake da kwallo 172, kuma shi ne na takwas a jerin wadanda suka fi zura kwallo, har ila yau saura kwallo 15 Salah ya kamo na hudu Andrew Cole – wanda zai iya kamowa a karshen kakar bana.
A wasan na ranar Lahadi, Salah ya kamo Dabid Becham wajen taimakawa a zura kwallo 80, inda yanzu su biyun suke mataki na 10. Yanzu yana bukatar taimakawa a zura kwallo 34 domin kamo Kebin de Bruyne, wanda shi ne biyu.
Wanda ya fi taimakawa a zura kwallo a gasar Premier League shi ne Ryan Giggs, wanda ya taimaka aka zura kwallo 162, amma ya fi Salah buga wasa da wasanni 353 kuma idan aka hada zura kwallo da taimakawa, Salah na gaba da shi. Ya sa hannu a zura kwallo 252 a wasa 279 a gasar Premier League, inda ya zama na bakwai a jerin wadanda jimillar zurawa da taimakawa a zura kwallo kuma idan ya ci gaba da yadda yake a yanzu, Salah zai kamo Alan Shearer a jimillar zurawa da taimakawa a zura, wato guda 324.
Yanzu dai abin da ake jira a gani shi ne, shin zai iya sabunta kwantiraginsa a kungiyar ta Liberpool? Kwantiraginsa dai zai kare ne a karshen wannan kakar kuma tuni kungiyoyi daga kasar Saudiyya suka fara bibiyarsa domin ganin ya koma can da buga wasa.