Rundunar ‘yansandan Jihar Katsina, ta bayyana cewa ta kashe ‘yan fashin daji 40 daga farkon shekarar 2024 zuwa Æ™arshenta.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, Aliyu Musa, ya bayyana hakan a yayin taron manema labarai na Æ™arshen shekara da aka gudanar a birnin Katsina a ranar Litinin.
- Atiku Ya Yi Allah-wadai Da Karramawar Da Sojoji Suka Yi Wa Seyi Tinubu
- Gwamnatin Kano Ta Samar Fursunoni Tsarin Kiwon Lafiya Kyauta
A cewarsa, rundunar ta ceto mutane 319 da aka yi garkuwa da su.
A cewarsa rundunar ta kuma kama mutum 916 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban.
“Mun samu nasarar tarwatsa gungun miyagu da dama, mun Æ™wato makamai, mun ceto mutanen da aka yi garkuwa da su, sannan mun gurfanar da wasu a gaban kotu,” in ji kwamishinan.