Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kammala shirye-shiryen kaddamar da rabon naira biliyan uku ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a daminar da ta gabata a jihar.
Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bayyana haka a lokacin da yake bayyana bude taron majalisar zartarwa ta jihar da aka gudanar yau a gidan gwamnatin Kano.
- Hukumar EFCC Ta Tsare Wasu Jami’anta 10 Bisa Zargin Karkatar Da Kayan Aiki
- Wakilin Musamman Na Xi Ya Halarci Bikin Rantsar Da Shugaban Ghana
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Laraba, ta ce, gwamna Yusuf ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ce ta bayar da tallafin ga jihohi 36 da babban birnin tarayya, a matsayin agajin bala’in ambaliyar ruwa na shekarar 2024.
Gwamnan ya kara da cewa, an tura kudaden ne zuwa asusun jihar a watannin da suka gabata a shirye-shiryen rabawa wadanda abin ya shafa.