ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tarihin Daular Borno Da Sarakunanta (3)

by Idris Aliyu Daudawa
11 months ago
Borno

An ambaci Kanem a daya daga cikin manyan dauloli uku a lardin Sudan wanda Ya’kubi yayi a shekarar 872.Ya yi bayani kan daular “Zaghāwa wanda ya zauna a wani wuri da ake kira Kānim”, wanda ya kunshi  wasu jihohin  vassal masu yawa.

“Wuraren da suke kwana a bukkoki ne wadanda aka yi da ciyawa ba kuma su da wasu Birane.” Suna zama da rayuwa ce kamar ta Fulani masu kiwo, yadda suke hakan ya basu dama suka zama ja gaba a vangaren soja. A karni na 10, al-Muhallabi ya ambaci Birane biyu a wata daula,daya daga cii sunanta Manan.

  • An Kashe ’Yan Ta’adda 34 Da Sojoji 6 A Harin Borno – Shalkwatar Tsaro
  • Tinubu Ya bayar Da Umarnin Bincike Kan Harin Da Boko Haram Ta Kai Wa Sansanin Sojoji A Borno

Sarkinsu an dauke shi wani babban al’amari, an yarda da shi ke bada ‘’rayuwa da mutuwa’’ “mai bada ciwo da lafiya”. Dukiya ana maganar ta da dabbobi, Tumaki,Shanu, Rakumma da kuma Dawakai.

ADVERTISEMENT

Daga Al- Bakri  a karni na  11 har zuwa abinda yayi gaba, ana kiran masarautar da sunan Kanem.A karni na 12 Muhammad al- Idris ya ambaci Mānān  a matsayin “wani karamin Birni wanda baya da masana’anta ko kuma harkar data shafi Kasuwanci”.Ibn Sa’id  al Maghribi ya kira Mānān a matsayiin hedikwatar Sarakunan Kanem a karni na 13 da kuma Kanem take da wani jarumin Sarki’.

Daular Saifawa shekarata (850 zuwa1846)

LABARAI MASU NASABA

Tsofaffin Ɗaliban BUK Sun Yaba Wa Masarautar Hausawan Turai Kan Naɗa Ma’ajin Hausawan Turai

Wakilin Gwale A Majalisar Kano Ya Zargi Magoya Bayan Sarki Aminu Da Cin Zarafinsa

Kanuri da suke musulmai sun samu damar shiga Kanem ne daga   mutanen Zaghawa wadanda masu kiwo ne a karni na 9 lokacin da aka samu matsalar . Wani mashahurin Kanuri ya bayyana cewa Sayf ibn Dhi Yazan shi ne ya samo daular Sayfawa. Sabuwar daular ita ce take rike da lamarin kasuwanci na Zaghawa a tsakiyar Sahara tare da Bilma da sauran wuraren da ake hakar gishiri.Sai dai duk da haka maganar kasuwancin shi ne lamarin Bayi. Kabilun da suke Kudu da tafkin Chadi an kai masu hari ko mamaya a matsayin Kafirun,daga can sai aka kai su zuwa Zawila a cikin Fezzan,inda ake bayar da mutane Bayi a bada Dokuna da makamai.A  ko wace shekara ana samun karuwar yawan Bayin da aka yi ciniki daga 1000 a karni na 7 zuwa 5000 a karni na 15.

Kamar yadda Richmond Palmer yace abin na al’ada ne a samu Mai yana zaune “Mai yana zaune ko ya zauna  kan wani abinda ake kira da suna  fanadir, dagil, ko tatatuna.Wani abin zama ne aka yi da fatar dabbar daji.”

Mai Hummay ya fara mulkin sa ne a shekarar 1075, inda ya kulla kawance da Kay, Toubou, Dabir,da Magumi.Shi ne Sarki musulmi na farko na daular Kanem, bayan da aka sa shi ya karbi shahada daga wurin Malamin shi Muhammad Man.Sai suka ci gaba da kasancewa tare a matsayin masu kiwo har zuwa karni na 11, lokacin da suka mai da hedikwatar zuwa Nijmi.

Humai shi ya gaji Dunama na 1 daga shekarar (1098 zuwa1151),ya yi aikin Hajji sau uku kafin ya samu matsalar data shafi ruwa a Aidab.A wancan lokacin, sojoji sun hada da 100,000 wadanda suke kan Dawakai da kuma sojoji zalla 120,000.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Alh. Hassan Baita Ubawaru (Ma'ajin Hausawan Turai)
Masarautu

Tsofaffin Ɗaliban BUK Sun Yaba Wa Masarautar Hausawan Turai Kan Naɗa Ma’ajin Hausawan Turai

July 31, 2024
Wakilin Gwale A Majalisar Kano Ya Zargi Magoya Bayan Sarki Aminu Da Cin Zarafinsa
Labarai

Wakilin Gwale A Majalisar Kano Ya Zargi Magoya Bayan Sarki Aminu Da Cin Zarafinsa

July 22, 2024
Tarihin Gusau Da Sarakunanta (2)
Masarautu

Tarihin Gusau Da Sarakunanta (2)

July 21, 2024
Next Post
Zamfara Ta Shirya Wa Kiwo, In Ji Ministan Bunkasa Kiwon Dabbobi

Zamfara Ta Shirya Wa Kiwo, In Ji Ministan Bunkasa Kiwon Dabbobi

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

December 21, 2025
Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

December 21, 2025
Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.