Assalamu alaikum masu karatu, barkanmu da sake haɗuwa da ku a wannan makon ta cikin shirin na mu mai farin jini da albarka na Adon Da Kwalliya.
A yau shafin na mu zai yi bayani ne akan yadda za ku gyara mamanku ya ciko ya yi vulvul.
Ki gyara dukiyar ki da kanki:
Abubuwan da za mu tattauna a cikin shirin namu:
Gyaran mama amarya wajan kwanciya.
Mene ne yake sa mama ya kwanta, kuma mene ne ke sa mama su zama ƙanana?
Gyaran mama a wajen kowacce mace kashi uku; Akwai maman da ya kwanta ake so su tashi su tsaya. Akwai ƙanana ana so su ƙara girma. Akwai kuma wanda girma suka yi da yawa ana so a rage.
Kuma yanzu za mu yi bayani a kan tsayuwar mama da kuma girmansu
Mene ne yake sa mama ya kwanta ?
Akwai yawan tsalle-tsalle, akwai yawan kama su, wani kuma maman haka yake yana da tsayi dama dole ya yi saurin kwanciya.
Sai kuma shekaru ( 35-40-50. )
Mene ne yake sa mama su zama ƙanana ?
Akwai hallita wata dama haka Allah yayita mamanta ƙanana ne.
Akwai wanda ake kwanciya a kansu. Akwai saka matsattsiyar rigar mama.
Ina za ki samu waxannan kayan haxin Islamic Medical Center. Ki tambaya amma waxansu kayan sai Kano (Kasuwar Kurmi ).
Yaya za’a gyara mama ƙanana ?.
Idan mamanki ƙanana ne kina so su yi manya kamar yadda kike so dai-dai, kina iya yin wannan haxin domin sanin lafiyar maman ki:
1 Cukwui. 2 Garin Alkama. 3 Aya. 4 Nonon Saniya ( Ko Madara ) 4 Garin Hulba ( Ko Man).
Cikwui wanda yawansa zai kai guda uku sai ki samu garin Alkama gwangwani xaya,sai Aya itama gwangwani xaya, sai ki daka su za su zama gari ki tankaɗe.
Ki samu nonon saniya idan kuma ba kya sha ki samu madara ki zuba wannan garin kamar cokali 3 ki dama kina sha kullum sau 1, sannan ki Lura lokacin da za ki yi wanka, ki tafasa ruwa da garin Hulba a ciki ki bari ya yi sanyi, sai ki wanke maman da shi, sannan ki yi wankan, wannan haxin matar aure wanda ta yi yaye za ta yi sannan budurwa za ta iya yi.
Kwanciyar mama:
Idan kuma kwanciya suka yi kina so su tsaya, sai ki nemo waxannan kayan za su tashi da yarda Allah.
Hulba, Ruwan ɗumi.
Ki kwava hulva da ruwan ɗumi, wato garin hulba ya xan yi kauri kar ya yi ruwa sosai, sai kin tabbatar kin gama abin da za ki yi.
Kin zo kwanciya sai ki shafa, ki kawo breziya xamammiya ki saka, da safe sai ki wanke da ruwan ɗumi, shima wannan matar aure za ta iya yi.
Za mu ci gaba mako mai zuwa