ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnan Zamfara Ya Yaba Wa Rundunar Tsaro Tare Da Jajanta Wa Al’ummar Da Harin Jirgin Sojin Ya Shafa A Jihar

by Sulaiman
2 years ago
Zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya yaba da ƙoƙarin da sojojin Nijeriya ke yi na kai hare-hare kan ’yan bindiga ba ƙaƙƙautawa a jihar.

A ƙarshen makon da ya gabata ne rundunar sojin saman Nijeriya ta kai wani samame kan ’yan bindigar da ke yunƙurin kai hari a ƙauyukan ƙananan hukumomin Zurmi da Maradun.

  • Hukumar CDC Ta Karyata Barkewar Sabbin Cututtuka Masu Yaduwa A Sin
  • An Nemi Sojoji Su Kara Jajircewa Wajen Gudanar Da Ayukansu

A wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Gusau, kakakin Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya jajanta wa iyalan fararen hula da harin da jirgin sama ya rutsa da su a Tungar Kara da ke ƙaramar hukumar Zurmi.

ADVERTISEMENT

Sanarwar ta ƙara da cewa, fararen hular da suka rasa rayukansu ’yan sintiri ne na yankin da aka yi zaton cewa ‘yan bindigar da suka tsere ne daga Gidan Makera a gundumar Boko a ƙaramar hukumar Zurmi.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Mun samu rahotanni masu inganci da yawa na farmakin da rundunar sojin sama ta Operation Fansar Yamma ta kai a ƙarshen mako a ƙananan hukumomin Maradun da Zurmi da ke fama da rikicin ’yan bindiga.

LABARAI MASU NASABA

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Zamfara

“Wannan farmakin da sojoji suke kaiwa ya rage wa ‘yan bindigar ƙwarin gwiwa matuƙa, ya kuma nuna aniyar rundunar sojojin saman Nijeriya na gudanar da aikin da Kundin Tsarin Mulkin ƙasar ya ba su na kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

“A matsayinmu na gwamnati mai kishin ƙasa, muna tabbatar wa ɗaukacin al’ummar jihar cewa, gwamnatin jihar Zamfara ta tsaya tsayin daka wajen ganin ta ci gaba da samun nasarori a yaƙi da ’yan bindiga. Nasarar da aka samu a baya-bayan nan na nuni da cewa ƙoƙarin haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro na jiha da na tarayya ya haifar da sakamako mai kyau.

“A bisa waɗannan nasarorin da aka samu, gwamnatin jihar ta sake jaddada aniyar ta na bayar da dukkanin tallafin da ya kamata ga rundunar sojin saman Nijeriya da sauran hukumomin tsaro domin ci gaba da gudanar da ayyukansu da kuma samar da zaman lafiya mai gorewa a jihar.

“Za mu ci gaba da ba da tallafi don inganta musayar bayanan sirri, samar da dabaru, da kuma ƙarfafa cuɗanyar da jama’a da jami’an tsaro, duk a bisa tsarin da ya dace na tabbatar da tsaro da kuma cimma burin maido da zaman lafiya a dukkan sassan jihar.

“Abin takaici, harin ya shafi wasu ’yan sintiri (JTF) a yayin farmakin a Tungar Kara, wanda ya yi sanadin asarar rayuka. Muna roƙon Allah Ta’ala ya saka musu da gidan Aljannah.

“Gwamnatin jihar na miƙa ta’aziyyarta ga iyalan jami’an JTF da suka mutu tare da ba su tabbacin cewa sadaukarwar da mamatan suka yi ba zai tafi a banza ba. Gwamnati za ta ba da tallafi da taimakon da ya dace ga iyalan waɗanda suka rasu.

Zamfara

“A ƙarshe, gwamnati na kira ga jama’a da su lura, su kai rahoton duk wani motsin da ba su gane masa ba, sannan su ba jami’an tsaro cikakken haɗin kai. Ta hanyar haɗin kai za a iya samun nasarar yaƙi da ‘yan bindiga tare da samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Zamfara.”

Zamfara
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan
  • Sulaiman
    ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
  • Sulaiman
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

MASU ALAKA

Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila
Manyan Labarai

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Next Post
Masallata Sun Kuɓuta Daga Harin Ƙunar Baƙin Wake A Jihar Borno

'Yan Ta'adda Sun Kashe Manoma 40 A Borno

LABARAI MASU NASABA

Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.