Karamin Ministan Manana’antu John Uwan-Enoh, ya bayyana cewa, kudurorin haraji da Gwamnatin Shugaban Kasa kirkiro da su, ne bisa nufin kara baunkasa tattalin arzikin kasar nan.
Owan-Enoh ya sanar da haka ne, a makon da ya gabata a taron manema labarai a Karamar Hukumar Etung, da ke a jihar Koros Ribas.
- Hisbah Ta Yi Kakkausan GargaÉ—i Tare Da Kira Ga Iyaye Kan Kula Da Yara Bayan Samun Gawar Wasu 4
- Xi Ya Zanta Da Babban Jagoran Vietnam Da Shugaban Sri Lanka
Kazalika, Uwan-Enoh, ya yabawa Shugaban Kasa Bola Tinubu kan kirkiro kudurorin harajin, inda ya sanawar da cewa, sauyin, zai taimaka wajen fannin matuka.
Ministan ya kuma tunasar da ‘yan Nijeriya kan alkawarin na Shugaban Kasa Bola Tinubu, na dala tiriliyan daya, don a kara habaka tattalin arzikin kasar, inda ya sanar da cewa, sauyin na daya daga cikin abinda Gwamnatin mai ci, ke burin cimma.
Uwan-Enoh ya ci gaba da cewa, ‘yan Nijeriya da dama, son soki wannan kudurorin na haraji, ba tare da sun yi dubi kan gundarin kudurorin ba, har ma ta kai ga wasun su, na yin kiraye-karaye ga Gwamnatin Tarayya na ta janye kudurorin.
Sai dai, Minitsna ya nuna jin dadinsa kan yadda wasu daga cikin masu kiraye-kirayen Gwamnatin na ta janye kudurorin, daga baya kuma suka fahinci manufar kudurorin, suka kuma nuna goyon bayansu akai.
Ya kara da cewa, Shugaban Kwamitin Tsara Kudurorin na Haraji na Fadar Shugaban Kasa Taiwo Oyedele, wanda kuma ya kayance ke jagorantar wanzar da kudurorin, yana kan gwaro da mari, wajen tattara akaluman da suka kamata dangane da kudurorin harajin.
Owan-Enoh, ya kuma bukaci ‘yan kasar da su marawa kudurorin na haraji baya, musamman don a gabatar da su, su zamo doka.
A ‘yan makwannin da suka gabata dai, kudurorin na harajin sun haifar da zazzafar muhawara daga lungu da sako na sassan kasar nan, duba da irin kalubalen da ake gani, za su haifarwa da tattalin arzikin kasar nan da kuma rashin dubi da bin ka’adaiar Shari’a wajen gabatar da kudurorin na harajin.
Kudurorin guda hudu, a yanzu dai, Shugaban Kasa Bola Ahamed Tinubu ya gabatarwa da Majalisar kasar, a watan Okutobar 2024.