A ranar 9 ga watan Yulin 2024, Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu; ya kaddamar da Kwamitin Fadar Shugaban Kasa, kan wanzar da sauye-sauye a fannin kiwon dabbobi a Nijeriya.
Manufar ita ce, domin cimma burin farfado da fannin kiwo a fadin kasar baki-daya, wanda aka kiyasata samun akalla Naira tiriliyan 33, duba da yadda a fanin ke bayar da gudunmawa kasa da kashi uku cikin dari ga tattalin arzikin wannan kasa a duk shekara.
- Kauyuka Suna Kokarin Neman Cimma Burin Samun Wadata Tare A Kasar Sin
- Yadda Kuncin Rayuwa Da Matsalar Tattalin Arziki Ke Kara Haifar Da Rikice-rikice Tsakanin ‘Yan Haya Da Masu Gidaje
Kasancewar Farfesa Attahiru Muhammadu Jega, a matsayin guda cikin shugabanin kwamitin tare da wasu kwararrun mutane 23, Shugaban Kasa Tinubu kuma da kansa ne ke jagorantar kwamitin.
Kazalika, an kuma gindayawa kwamitin sharudda 16 na wanzar da sauye-sauye a fannin tare kuma da zamanantar da fannin na kiwo.
A rahoton farko, a bangaren rahoton Jega; ya bayar da wasu shawarwari, domin farfado da fannin; ciki har da kiwon don samun riba.
A bangaren kiwon Kajin gidan gona, rahoton ya kiyasta tsintsayen da ake kiwo da suka kai kimanin miliyan 563, inda kwamtin ya shawarci gwamnatin tarayya da ta tallafa wa masu kiwon kajin gidan gonar su kimanin 185,000, da kayan aiki ga kanannan masu kiwon kajin gidan gona.
Kazalika, rahoton ya bayar da shawarar taimaka wa masu kiwon kaji kimanin 550,000; da sauran kungiyoyin da ke kiwon, wanda adadinsu ya kai 735,000.
Bugu da kari, rahoton ya kuma bayar da shawarar kula da saurin jinsin kajin cikin gidan da ake kiwatawa tare da samar da kayan aikin da ake adana naman da ake amfani da shi a cikin kasar.
Rahoton ya kuma shawarci gwamnatin, ta kara habaka fannin kiwon kasar tare da kara karfafa kasuwancin fannin da suka hada da Cibiyar Bunkasa Binciken Kiwon Dabbobi da ke Garin Shika a Jihar Kaduna da sauran makamantansu.
Rahoton ya kuma shawarci gwamnatin, ta kirkiro da shirye-shiryen kiwon kajin gidan gona da samar da kayan zamani na gwajin lafiyar dabbobin tare kuma da samar da rijiyoyin burtsatsai da fitilu masu aiki da hasken rana a wuraren da masu kiwon kajin gidan gonan suke tare da samar da sassan kyankyasar kwan kajin gidan gona.
Kazakila, rahoton ya kuma bukaci a kara daga darajar kiwon kamar irin su Talo-talo, Agwagi, Tantabaru, Jimina da sauran makamantansu.
Rahoton ya kuma yi nuni da cewa, yin amfani da wadannan shawarwari, za su taimaka wajen kara samun masu zuba hannun jari a fannin na kiwo a kasar.
Har ila yau, rahoton ya kuma bayar da shawara tare da kirkiro da cibiyar gudanar da bincike kan kiwon kajin gidan gona, wacce za ta ksanace daya daga cikin sabbi guda takwas na cibiyoyin gudanar da bincike.
Kazalika, rahoton ya shawarci gwamnatin da ta kara daga darajar cibiyar gudanar da binciken kiwon dabbobi ta kasa (NAPRI) tare kuma da kara daga darajar cibiyar gudanar da bincike, kan kula da lafiyar dabbobi ta kasa (NBRI).