Mataimakin shugaban kasar Sin Han Zheng, ya ce a shirye Sin take ta hada hannu da Amurka karkashin tsarin diplomasiyya domin aiwatar da matsayar da shugaban Sin Xi Jinping da zababben shugaban Amurka Donald Trump suka cimma, ta yadda za a ingiza ci gaban dangantakarsu cikin aminci.
Han Zheng ya bayyana haka ne yayin ganawarsa da zababben mataimakin shugaban kasar J.D Vance a jiya Lahadi. Yanzu haka, Han Zheng na birnin Washington domin halartar bikin rantsar da shugaba Trump yau Litinin, a matsayin wakilin musammam na shugaba Xi.
Yayin ganawarsa da wakilan ‘yan kasuwar Amurka, Han Zheng ya ce suna fatan kamfanonin Amurka za su ci gaba da zuba jari da samun matsuguni a kasar Sin, tare da taka muhimmiyar rawa a matsayin gadar da za ta bayar da gudunmuwa ga raya dangantakar kasashen biyu cikin aminci. (Fa’iza Mustapha)