ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ayyukan ‘Yan Ta’adda Na Barazana Ga Shirin Gwamnati Na Wadata Kasa Da Abinci

by Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
1 year ago
Barazana

Kokarin da gwamnatin Tarayya ke yi na wadata kasa da ‘yan kasa da abinci na ci-gaba da fuskantar mummunar barazana daga ‘yan ta’adda da ke hanawa manoma noma musamman a yankin Arewa. 

‘Yan ta’addan wadanda suka dauki tsayin shekaru suna cin karensu ba babbaka ba tare da gwamnati ta kawo karshen su ba, sun jima suna hanawa manoma noma abinci a gonakin su wanda hakan ke haddasa karancin abinci.

  • Dutsen Da Amurka Ta Jefa Ya Fado Kasa
  • ’Yansanda Sun Ceto Ɗan Ghana, Sun Kama Masu Garkuwa Da Mutane 3

Dubun- dubarar manoma sun rasa amfanin gona na biliyoyin kudade a dalilin gagarumar illar da barayin daji ke yi masu a kowace kakar noma ko dai ta hana masu noma, tilasta su biyan haraji ko kone amfanin gonan a lokacin da suka kammala wahalar aikin gona.

ADVERTISEMENT

A bisa ga muhimmancin aikin gona, Gwamnatin Tarayya ta kebe naira bilyan 826.5 a matsayin kasafin kudin ma’aikatar gona da samar da abinci na wannan shekarar 2025.

Kasafin kudin ya karu a bisa ga na shekarar da ta gabata wato naira bilyan 362.da karin kashi 128%..Sai dai masana aikin gona na ganin kasafin ya yi karanci wajen magance kalubalen karancin abinci a kasar nan.

LABARAI MASU NASABA

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

Gwamnatin Nijeriya na da shiraruwa da dama da manufar wadata kasa da abinci, inganta samun kudin shiga a karkara da rage fatara ta hanyar shiraruwa masu dorewa na bunkasa aikin gona, sai dai a kodayaushe kalubalen ‘yan ta’adda na hana shiraruwan samun nasara.

Rahotanni da dama sun ruwaito yadda ‘yan ta’adda ke tilastawa manoma biyan haraji gabanin su ba su damar shuka da girbe amfanin gona a gonakin su wanda hakan babban kalubale ne ga manoma da kasa bakidaya.

A bisa ga kasa biyan harajin da barayin dajin ke tilasta masu, dimbin manoma sun rasa rayukan su wasu kuma da dama sun yi gudun hijira daga garuruwan su domin tsira da rayukan su.

A watan Yuni da ya gabata kadai jagoran ‘yan ta’adda, Bello Turji ya bayyanawa manoma za su iya noma ne kawai cikin kwanciyar hankali idan suka biya harajin naira miliyan 50.

Kudin fansar da ya kakaba masu ya shafi manoma ne a tsallaken Gulbi daga kauyen Fakai a karamar hukumar Shinkafi da ke jihar Zamfara zuwa Kaya bakin iyaka da kasar Nijar.

Biyan haraji tuni ya riga ya zama tamkar al’ada ga manoma a wuraren da ke da hatsarin ‘yan ta’adda a Arewa domin su samu damar gudanar da shuka da girbi ba tare da wata matsala ba.

Duk da haka a lokutan baya rahotanni sun tabbatar da rasa rayukan manoma da dama bayan biyan harajin a yayin da a wasu lokutan suke rasa amfanin gona ga ‘yan ta’addan ko kuma a yi biyu babu bakidaya.

Bincike ya nuna bukatar ‘yan ta’addan ta fi kamari ne a jihohin Zamfara, Neja, Katsina, Kaduna, Sakkwato da Benue a inda manoman kan hadu da fushin ‘yan ta’addan idan suka sabawa umurnin su ta hanyar kona amfanin gonar tare da kai masu hari a garuruwan su.

A bisa ga wannan jama’a da dama sun watse a garuruwa da dama a bisa ga kasa iya biyan harajin da barayin dajin suka tilasta masu wanda gudun hijira ne kadai mafitar tsira da rayukan su.

Wani manomi kuma shugaban al’umma a Katsina da ya bukaci a sakaya sunansa ya bayyana cewar harajin da barayin dajin ke saka masu a wasu lokutan yana da yawan da babu riba idan aka hada da abin da suka shuka wanda a kan hakan manoman da ke fuskantar barazanar ke kauracewa gonaki.

“Akwai mamakin sanya harajin naira miliyan biyar ga manomin da gonar sa ba za ta kai miliyan biyu ba kuma a mafi yawan lokuta akan hada manoma da yawa a sa masu biyan harajin. Harajin da za ka biya a wasu lokutan ya danganta da yanayin abin da ka shuka. Kisa ne hukuncin rashin biya tare da lalata amfanin gonar da kai mana kazamin hari.”

Ya ce hare- haren ta’addanci da barayin daji ke kaiwa a gonaki tare da lalata amfanin gona da aka girbe na kara sanya damuwa kan makomar kasar nan wajen samar da wadataccen abinci.

Ta’addancin wanda kai tsaye ake kaiwa ga amfanin gona ya kara bayyanar da kasawar Nijeriya a fannin noma ta hanyar saka miliyoyin jama’a a cikin barazanar yunwa. Da yawan manoman da suka fuskanci kalubale gabanin kammala noma, kan hadu da kunar zuciya yayin cire amfanin gona.

Kafafen yada labarai sun ruwaito yadda ‘yan ta’adda suka kunnawa masarar da aka cire wuta a kauyen Kwaga da unguwar Zako duka a karamar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna tare da barin manoman cikin mawuyacin hali.

Ire- iren makamancin wannan harin da ‘yan ta’adda ke kaiwa a gonaki su kone amfanin gona bakidaya bayan an riga an girbe a na shirin kaiwa gida da kasuwa ba bakon abu ba ne ga manoma musamman a yankin Arewa.

A damanar da ta gabata daga Arewa ta tsakiya zuwa Arewa maso- yamma an samu munanan rahotanni kan yadda hatsabibin ‘yan ta’addan ke gallazawa manoma ta hanyar kone gonakin gero, masara, dawa da wake da sauran amfanin gonar da aka riga aka yi girbi wanda ya girgiza gwamnati da Majalisar Dinkin Duniya.

Wannan aika- aikar da ta faru tuni Majalisar Dinkin Duniya a karkashin shirin ta na samar da abinci da shirin duniya na samar da abinci da ma’aikatar gona da samar da abinci ta tarayya da sauran abokan hulda suka yi hasashen cewar mutane miliyan 33 a jihohi 26 da Birnin Tarayya za su fuskanci karancin abinci a tsakanin Yuni da Agusta wannan shekarar 2025.

Jihohin da hasashen ya bayyana zai shafa sune Kaduna, Zamfara, Sakkwato, Borno, Adamawa, Yobe, Gombe, Taraba, Katsina, Jigawa, Kano, Bauchi, Filato, Kebbi da Neja.

A yayin da gwamnati ke kashe makuddan kudade domin ganin ta samu nasarar wadata kasa da abinci, a kuma daidai lokacin da ‘yan ta’adda ke yi wa shirin zagon kasa babban nauyin da ke kan gwamnati shine daukar kwararan matakan yakar ayyukan ta’addanci da dukkan karfin ta domin samar da zaman lafiyar da za ta baiwa al’umma sukunin yin noma da wadata kasa da abinci a cikin kwanciyar hankali.

Barazana
Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
+ postsBio
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    2027:Cece-kuce Ta Barke Tsakanin Tinubu Da Atiku
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Yadda Rikici Ya Tsananta Tsakanin Dan Daba Da Malaman Addini A Sakkwato
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Dalilin Yawaitar Haduran Kwale-kwale A Yankin Sakkwato
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Atiku Ya Koka Kan Ƙaruwar Ta’addanci A Sakkwato

MASU ALAKA

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi
Manyan Labarai

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

September 9, 2026
Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa
Labarai

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

September 9, 2026
Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila
Manyan Labarai

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
Next Post
Maraba Da Shekarar Hijirah Ta 1447: Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar (1)

Maraba Da Shekarar Hijirah Ta 1447: Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar (1)

LABARAI MASU NASABA

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

September 9, 2026
Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

September 9, 2026
Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.