Kamfanin NNPCL ya ƙara farashin litar man fetur a gidajen man da ke Abuja da Jihar Legas.
A gidajen mai mallakin NNPCL, farashin lita ya tashi daga naira 960 zuwa 990, yayin da a gidajen man ƴan kasuwa ya kai Naira 1,030.
- Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin: Babu Wanda Zai Ci Nasara A Yakin Cinikayya Ko Yakin Harajin Kwastam
- DSS Ta Maka Mahdi Shehu A Kotu Kan Zargin Ta’addanci
Wannan ƙarin ya sa farashin ya zarce na matatar Dangote, wanda ke fitar da litar mai a kan Naira 955 tare da haɗin gwiwa da gidajen mai irin su MRS, Ardova, da Heyde.
A ranar 17 ga watan Janairu, Matatar Dangote ta sanar da ƙara farashin man da ta ke fitarwa, wanda ya fara shafar gidajen mai.
A Legas, rahotanni sun nuna cewa a ranar Talata, farashin lita a gidajen mai mallakin NNPCL ya tashi daga Naira 925 zuwa 960.