Asibitin koyarwa na Aminu Kano (AKTH), ya musanta zargin cewa ma’aikatansa sun cire mahaifar wata majiyyata ba tare da izininta ba a lokacin haihuwa, tare da bayyana iƙirarin a matsayin zargi mara tushe da yunƙurin zubar da ƙimar asibitin a idon duniya.
Wannan na zuwa be bayan da wata mata ta fito a wani shahararren gidan radiyo da Talabijin mai suna ‘Berekete Family’, inda ta yi zargin cewa a shekarar 2017 yayin haihuwa a AKTH, an cire mahaifar ta ba tare da saninta ba, wanda labarin ya dauƙi hankali musamman a shafukan sada zumunta, wanda ya ake wa babban asibitin kallon yayi sakaci.
- ‘Yan Bindiga Sun Harbi Likita Tare Da Garkuwa Da Ma’aikatan Jinya A Wani Harin Asibiti A Katsina
- Gwamnatin Tarayya Ta Musanta Zargin Bai Wa Kamfanin Bogi Kwangilar Aikin Hanyar Abuja-Kano
A cewar matar, a shekarar 2017 ne aka kwantar da ita a AKTH domin ta haihu, ba da dadewa ba ta fita a hayyacinta amma bayan kwana shida da ta farfado aka sanar da ita cewa jaririn ya mutu ba, kuma an cire mahaifarta ba tare da tuntubar ta ba.
Amma martaninsa, babban daraktan AKTH, Dr. Abdurrahman Abba Sheshe, ya ƙaryata zargin, inda ya bayyana cewa cire mahaifar nata ya zama dole a lokacin domin ceton ranta saboda babbar barazanar da ke tattare da ita.
Dokta Sheshe, ya ci gaba da cewa an samu amincewar aikin tiyatar cire maiharfar, tare da yin watsi da ikirarin cewa an cire mahaifar ne ba tare da amincewar majiyyaciyar ba, inda ya kira hakan wani yunkurin ɓatanci da aka shirya wa domin ɓata sunan asibitin.
Sai dai asibitin ya ƙi fitar da kwafin fom ɗin amincewa ko bayyana ainihin wanda ya sanya hannu kan tiyatar cire mahaifar, lamarin da ya ƙara rura wutar raɗe-raɗin da jama’a ke yi game da rashin da’a da karya dokar aiki.