A duk ranar 15 ga watan Janairu na kowace shekara ne, a Nijeriya, ake gudanar da bikin tunawa da zagayowar ranar dakarun sojujin Nijeriya mazansu da matansu, ‘yan mazan jiya.
A saboda haka ne, yana da matukar mahammianci mu yi waiwaye kan irin sadaukarwar da suka yi ta rayuwarsu, wajen tabbatar da zaman lafiya da hadin kan kasar, musamman ma idan aka yi la’akari da cewa, sun fafata yakin duniya na daya da na biyu da kuma a lokacin yakin basasar Nijeriya.
- A Shirye Kasar Sin Take Ta Kyautata Dangantakar Tattalin Arziki Da Amurka
- Shirin Tallafinmu Ga Nijeriya A 2025 Zai Kai Ga Asalin Mabukata – Wakilin MDD
Ana iya tunawa, kasar Ingila ce, ta reni Nijeriya ta kuma bata ‘yancin kai, a baya ana kara tunawa da zagayowar ranar ce, a ranar 11 na kowane watan Nuwamba, musamman ma domin tuna kawo karshen yakin duniya na farko
Sai dai kuma, bayan da waccen Gwamnatin mulkin soji ta samu galaba a kan dakarun sojojin masu yunkurin kafa kasar Biyafara a ranar 15 ga watan Janairun 1970, aka sauya ranar da gudanar da bikin daga cikin Kalandar kasashen renon Ingila wato Commonwealth, zuwa ranar 15 ga watan Janairun domin, a rinka tunawa da yakin na basasa.
Shekaru aru-aru, dakarun sojojin mu, sun sadaukar da rayukansu wajen kare karfin ikon Nijeriya, rayukan ‘yan kasar, don tabbatar da zaman lafiya da kuma ci gaba da wanzuwar Nijeriya.
Kazalika ma, sadaukar da kansu da kwarin gwiwarsu na fuskantar dukkanin wani hadarin yaki, wanda hakan ya sanya aka ci gaba da nuna godiya a gare su, da kuma girmama su, a daukacin fadin kasar mu.
Hakan ta sa abin ya zama mana wajibi, mu ci gaba da tuna su da kuma girmama su, la’akari da sadaukar da kan da suka yi ga kasar mu.
Hadurun da suka fuskanta, a zahirance suke, in aka tuna da yadda suka rasa rayukansu, wajen yakar ‘yan ta’adda da sauran masu aikata manyan laifuka, da suka zamo barazana, ga tsaron kasar.
Amma a nan, tunanin mu, ya karkata ne, zuwa ga iyalansu da suka rasu suka bari, abokan arzikinsu da kuma yankunan da suka fito.
Bisa sadaukar da rayukansu da suka yi ne, hakan ya sanya muka ci gaba da zama a cikin zaman lafiya muka kuma ci gaba da gudanar da ayyukansu, na yau da kullum.
A saboda haka ne, akwai babban bashi da yake a kanmu, na ci gaba da tunawa da su, tare da kuma girmama su.
A yayin da muke gudana da bikin tuna su, ya zamar mana wajibi mu taimakawa sauran dakarun ‘yan mazan jiya da ke raye da kuma sauran dakarun da a yau, suke ci gaba da nauyin ba Nijeriya kariya.
Bugu da kari dakarun namu suna ci gaba dayin aiki tukuru wajen tunkarar dukkan wata barazana daga wurin ‘yan ta’adda, ‘yan fashin daji, masu satar danyen mai da sauran masu aikata manyan laifuka, a kasar.
Abin jin dadi ne, matuka, musamman irin dimbin ci gaban da ake ci gaba da samu, musamman yadda, rundunar tsaron kasar ta ruwaito cewa, dakarunta da ta tura masu dakile aikata ta’addanci, a wasu ayyukan da suka kaddamar, sun kashe ‘yan ta’adda 109, tare da kuma cafke wasu 81 a makon farko na 2025.
Daraktan sashen yada labarai na rundunar Manjo Janar Buba Edward, ya sanar da cewa, “A cikin makon dakarun sun hallaka ‘yan ta’adda 109 tare da kama wasu 81 da kuma ceto wasu mutanen da aka yi garkuwa da su 43.”
Sai dai, a bisa ra’ayin wannan jaridar, duk a wannan dimbin nasarorin da aka samu, akwai sauran manyan kalubale.
Wasu rahotannin suna bayyana cewa, akalla mutane 77 ne, aka kashe tare da kuma yin garkuwa da mutane 43, hakan ya biyo bayan hare-hare da aka kai daban daban a jihohi 10, a cikin mako biyu kacal, da suka wuce.
An kuma kone gidaje da dama, tare da tarwatsa mutane sama da 1,000, daga matsugunansu.
Bugu da kari kuma wasu dakarun soji shida, sun rasa rayukansu, a wani harin na ‘yan ta’adda, a ranar 4 ga watan Janairu 2025.
Sun rasa rayukansu ne, a yayin da maharan suka kai hari a sansanin soja da ke a Sabon Gida, Damboa a jihar Borno.
Bayan kai wannan harin, Shugaban kasa Bola Tinubu, ya bayar da umarnin da a gudanar da cikakken bincike, tare da kuma yabawa rundunar sojojin kasar kan daukar matakin gaggawa da ta yi, musamman wajen kai hare-hare da Jiragen yaki na sama a kan sansanin ‘yan ta’adda, wanda hakan ya janyo aka kashe su da dama.
Dole ne mu rinka bai wa dakarun sojojin mu kariyar da ta kamata da kuma kulawa da jin dadinsu da walwalarsu da kula da kiwon lafiyarsu tare da kuma biyan bukatun iyalansu.
Jajirtattun sojojin da suka dawo daga fagen daga/fama,dole ne a samar masu da gidaje, samar masu da damar samun daukar aiki, domin a karrama su, bisa gudunmawar da suka bayar ta sadaukar da kansu,wajen dorewar tsaro da wanzuwar kasar Nijeriya.