Al’ummar Duniya ta ware ranar 30 ga watan Yuli na kowacce shekara don fadakar tare da tunatar da al’umma illar safarar mutane a duniya.
Wannan abin kyamar ya samo asali ne ga yadda aka tsani yadda ake gudanar da safarar mutane a matsayin bayi a shekarun baya kuma, duniya ta dauki matakin watsi da wannan sana’ar musamman ganin yadda ake cin zarafin mutanen da aka yi safararsu tare da kuma ci da guminsu.
- Wang Wenbin: Hannuwan ‘Yan Siyasar Amurka Da “‘Yan Ina Da Yaki” Na Jike Da Jinin Al’ummun Gabas Ta Tsakiya
- Yadda Rijiya Ta Rufta Da Uba Da Ɗansa A Kano
Taken bikin na wannan shekarar shi ne yadda ake amfani da kafafen sadarwa na zamani wajen amfani da su don safarar mutane a sassan duniya da nemo hanyoyin dakile harkokin masu safarar mutane.
Majalisar dinkin Duniya ta bayar da shawarar daukar matakin fadakar da jama’a bukatar taka-tsantsan wajen amfani da kafafen sadarwa na zamani don kaucewa fadawa tarkon masu safarar mutane wadanda suke amfani da jahilcin mutane wajen cutar da su.
Ana sa ran amfani da taken na wannan shekarar don fito da dukkan hanyoyin da masu safarar mutane za su iya amfani da su wajen aiwatar da mugun aikin nasu tare da fadakar da al’umma hanyoyin kauce wa fadawa tarkon nasu.
“Masu safarar mutane na amfani da kafafen sadarwa wajen yaudarar mutane ciki har da yara kanana, suna amfani da hanyoyi dabandaban don jawo hankalin mutane, kamar yadda Majalisar dinkin duniya ta ankarar.
“Haka kuma masu safarar mutane na amfani da sirrikan kafafen sadarwa wajen hulda a tsakanisu ba tare da al’umma sun fahimci abin da ake ciki ba suna kuma ankarar da junansu don kaucewa fadawa hannun jami’an tsaro.”
A jawabinsa na wannan ranar, Shugaban Majalisar dinkin Duniya, Antonio Guetteres, ya bayyana cewa, wadanda suka fi fadawa komar masu safarar mutane sun hada da mata da yara kanana.
“Masu safarar mutane na amfani da rauninsu ta hanyar amfani da kafofin sadarwa na zamani tare da kwarewarsu na kimiyya da fasaha wajen bibiya tare da yaudarar mutane, sukan kuma kwadaitar da su samun ayyuka a kasashen waje.”
Hukumar majalisar dinkin mai kula da masu aikata manyan laifufkka (UNODC) a rahotonta na shekarar 2018, ta bayyana cewa an samu nasarar gano akalla wadanda aka yi safarar su har mutum 50,000 da aka bayar da rahoton su a kasashe 148.
Haka kuma an fahimci cewa, kashi 50 na wadanda aka yi safarar na su ana yi ne don sanya su a sana’ar karuwanci a kasashen duniya, kashi 38 kuma ana jefa su ayyukan karfi ne ba tare da albashi ba.
An kuma gano cewa, kashi 46 daga cikin wadanda aka yi safarar nasu mata ne yayin da kuma kashi 19 kananan yara mata ne.
Daya daga cikin mutum uku daga wadanda aka yi safarar su suna kasancewa yara ne kanana yayin da kuma yawan yaran da ake safarar yana karuwa a kullum haka kuma yawan yara maza da aka yi safara su a cikin shekara 15 ya karu da kashi 5 a fadin duniya a ‘yan shekarun nan.
Majalisar ta kuma sanar da cewa, rahotanni ya nuna cewa, kashi 79 na wadanda ake safarar ana yin hakan ne don jefa su ayyukan karuwanci.
An kuma fi farauto ‘yan mata don amfani da su wanannan sana’ar. A rahotonta na shekarar 2021, hukumar yaki da safarar mutane a Nijeriya (NAPTIP), ta bayyana cewa, an samu rahoton safarar mtane har 1,112 yayin da kuma kashi 35.8 a cikin su an farauto su ne don abin da ya shafi harkar karuwanci da zama bakin haure.
Haka kuma rahoton UNDC na shekarar 2020 ya nuna cewa, kashi 60 na wadanda aka yi safarar su yankin Afrika Yamma yara ne kanana, an kuma karfafa matakai don kawo karshen wananan lamarin da gaggawa.
Yawancin masu safarar na fakewa ne da halin talauci da al’umma ke ciki ne wajen yaudarar mutane wadanda suke fafutukar tserewa daga kangin talaucin da suke fuskantar da kuma barazana na rayuwa a fannoni da dama kamar yadda kungiyar Lauyoyi Mata ta duniya (FIDA) ta bayyana a taron kwanakin baya.