“Wannan dai ya wuce sai a kiyayi gaba, muma kuma mu yi hakuri,” in ji Sha’eeratu. Shahida ta ce; “Ai na san ba zai jima ba zai dawo, kuma za mu dinga ziyartar ki sa’i-sa’i, ni dai na koma gida.”
Shi kuwa Shahid bayan ya dawo daga juma’a ya wuce gida ya ci abinci, kana ya kwanta ya yi bacci, da lokacin Sallar La’asar ya yi sai ya tashi bisa isharar tsuntsunsa Hafir ya je ya ba da farali.
- Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutane 3, Ta Rushe Gidaje 495 A Kano
- CDD Ta Soki NBC Kan Cin Tarar Trust TV Da Wasu Miliyan 20
Hafir wani aku ne da Shahid ya karve shi a wurin mahaifinsa, a duk sa’adda yake bukatar a tashe shi daga bacci shi ne yake tashinsa, haka zalika idan yana bukatar ya tuna masa wani da zai yi, to sai ya gaya wa Hafir, shi kuwa da lokacin ya yi sai ya tuna masa da irin yanayin da zai gane.
Bayan an yi Sallar La’asar ya wuce zuwa gidan Sarki, don ya sanar da Samirul’adalasi abin da ya faru, da ya same shi suka zauna Samirul’adalasi ya dube shi “Shahid na ga fuskarka da alamar damuwa,” Shahid ya ce; “A a daga bacci na tashi, amma dai akwai damuwa, sai dai damuwar kadan ce tun da ka fini sanin abin da zai faru, kuma dama ka fada min kafin afkuwarsa.
Na je wurin Hafida tun kusan lokacin Walha, amma ban samu ganin ta ba, har lokacin Sallar juma’a, da na ga lokaci ya yi na hakura na dawo gida.”
“Wannan kadan kenan daga cikin halinta kamar yadda na ambata maka.” Na bar mata sakon tafiyata, duk da ban fadi ranar da zan koma ba, amma dai nan da makonni biyu zan koma, sannan na san ta fidda rai da zuwana.” Wannan shi ne lamarin Samirul’adalasi da abokinsa Shahid.
Ita kuwa Hafida, kullum sai ta yi kwalliya mai tsananin kyau, sannan a ko da yaushe dakinta a cike yake da kawaye don sauraron dawowar bakonta, amma ina shiru babu labarinsa.