Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya maka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, kan tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a 2023.
A cikin karar, Gwamna Wike, da wani jigo a PDP da kuma wani, Michael Ekamon, an lissafo su a matsayin masu shigar da kara bi da bi.
- Rikicin PDP: Ba Za Mu Bai Wa Wadanda Ba Sa Kaunar Ribas Kuri’unmu Ba – Wike
- Me Ya Sa Ake Rubibin Wike A Siyasar Nijeriya?
Sauran wadanda ake tuhumar sun hada da Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto da kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).
A cewar bayanan kotun, an yi amfani da dukkan matakai akan dukkan bangarorin da ke cikin lamarin.
Wike ya roki kotun da ta duba yuyuwar tsige Tambuwal ya daga mukaminsa saboda rashin sauka daga kujerarsa lokacin zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar PDP ko kuma ya rasa kuri’unsa.
Wike da Ekamon sun yi zargin cewa idan har za a tantance batutuwan da suka dace, kotu ta ba da sassauci har guda tara da suka hada da bayyana cewa za a soke zaben Tambuwal na kuri’un Atiku.
Masu shigar da karar sun kuma nemi a bayyana cewa PDP ta yi sakaci da rashin tausayi ta hanyar baiwa Atiku kuri’un gwamnan jihar Sokoto a zaben fidda gwani da aka gudanar a babban taron jam’iyyar PDP na kasa a watan Mayu, 2022.
Sun roki kotun da ta soke zaben da kuma umarnin da ya hana wanda ake kara na 3 (Tambuwal) janyewa a zaben fidda gwani bayan an fara kada kuri’a.
Masu neman takarar sun kuma roki kotun da ta bayyana cewa PDP da Atiku sun yi amfani da damar da ba ta dace ba wajen janyewar Tambuwal a lokacin da suka baiwa gwamnan Sokoto damar neman kuri’un wakilai masu zabe da su zabi tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku a wannan zaben.
Wike da Ekamon sun roki kotun da ta umurci INEC da ta ki amincewa ko ta cire Atiku daga cikin ‘yan takararta a zaben shugaban kasa na 2023.
Suna kuma neman kotun da ta bayar da umurnin jam’iyyar PDP da ta sake kidaya kuri’un zaben fidda gwani da aka gudanar a ranakun Asabar 28 ga watan Mayu da kuma Lahadi 29 ga watan Mayun 2022.