Ministan Ma’aikatar Bunkasa Kiwo, Idi Mukhtar Maiha ya bayyana cewa, aikin gina mayankar dabbobi ta rukunin kamfanonin ABIS da ke Abuja, baya ga taimakawar da za ta yi wajen sarrafa Nama, za kuma ta taimaka wajen samar da ilimi a fadin kasar nan.
Da zarar an kammala aikin mayankar, za ta taimaka wajen kara bayar da dama a bangaren zuba hannun jari tare kuma da tallafa wa mayankar da ke Jihar Legas, wajen sarrafa Naman Shanu 200 a kowace rana da sarrafa Naman Kajin gidan gona 15,000 da kuma sarrafa tan 100 na Kifi.
- Abin Da Ya Sa Masu Ruwa Da Tsaki Suka Gana Da Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur
- Wakilin Musamman Na Shugaba Xi Zai Halarci Taron Koli Kan Fasahar AI A Faransa
Kazalika, idan an kammala mayankar, za a iya sarrafa Shanu 1,000 tare da samar da tan daga 400 zuwa 600 na Kajin gidan gona da Awaki 2,000 da Raguna tan 1,000 na Kifi da sauran makamantansu.
Wannan zuba hannun jari na dala miliyan 30, zai samar da ayyukan yi na kai tsaye kimanin 1,000, tare kuma da samar da ayyukan yi wadanda ba na kai tsaye ba, sama da 20,000 a fannin kiwo a wannan kasa.
Maiha, a jawabinsa lokacin da ya kai ziyarar aiki ga mayankar ta ABIS da ke yankin Idu a Abuja, ya sanar da cewa; karancin da ake da shi na kwararrun masu kula da fannin kiwon dabobi a kasar, nan ba da jimawa ba; zai zama tarihi.
A cewar Maiha, kafa wajen bayar da horo da kamfanin na ABIS ya yi, zai cike gibin da ake da shi a fannin kiwo da kuma bayar da gudunmawa wajen kara habaka tattalin arzikin fannin.
Ministan ya kara da cewa, bayar da ingantaccen horo a fannin bunkasa kiwo, zai taimaka wajen samar da wadataccen abinci da kara samar da ayyukan yi ga ‘yan kasar, musamman ma matasa.
Maiha, ya kuma bai wa kamfanin na ABIS tabbacin cewa, ma’aikatarsa, za ta bai wai kamfanin goyon bayan da ya dace, domin samar da kwararru a fannin bunkasa kiwon kasar.
Da yake yin tsokaci kan jajircewa da mayar da hankali na kamfanin na ABIS, Maiha ya bukaci kamfanin ya yi hadaka da ma’aikatarsa, musamman domin cimma burin da ya sanya a gaba na sarrafa Nama a kasar.
Ya kuma jaddada cewa, fannin kiwo na matukar taimakawa wajen samar da ayyukan yi da kuma kara habaka tattalin arzikin kasa.
Shi kuwa a nasa jawabin, Shugaban kamfanin na ABIS, Jakada Emmanuel Nelson Usman ya bayyana cewa, an kafa kamfanin ne, domin yin amfani da kimiyyar zamani; wajen sarrafa Nama a kasar.
Ya sanar da cewa, ta hanyar kamfanin; za a iya samar da ayyukan yi na kai tsaye da kuma wadanda ba na kai tsaye ba ga ‘yan kasar, wanda hakan zai taimaka wajen kara habaka tattalin arzikin kasar da kuma kara samar da wadataccen abinci a Nijeriya.
Nelson, ya kuma bukaci taimako daga Ministan Ma’aikatar Bunkasa Kiwon, musamman a bangaren sahalewar shigo da sundukan kamfanin da ke dauke da kayan kamfanin ta hanyar tashoshin jiragen ruwa na kasa, musamman don kamfanin ya samu damar kafa makarantar koyar da kiwon dabbobi.