Malam Inuwa, daya ne daga cikin dattawa a Masana’antar Kannywood, wanda ya ce, ya fara harkar wasan kwaikwayo, tun kafin zuwan masana’antar ta Kannywood.
Har ila yau, ya bayyana yadda rawa ta canza da kuma yadda shi kansa kidan ya canza a wannan masana’anta, wanda ya bayyana cewa; yanzu ne take cike da mutanen arziki da ke samun arzikin duniya da kuma na lahira, ba kamar a lokacin baya ba.
- A Shirye Nake Na Tattauna Da Shugaban Rasha – Zelensky
- An Kaddamar Da Cibiyar Ilimin Fasahar Zamani Ta Sin Da Afirka A Jami’ar Kenya
Inuwa, a wata tattaunawa da ya yi da jaruma Hadiza Gabon, a cikin shirinta na ‘Gabon’s Room Talk Show’, ya bayyana yadda tun kafin zuwan kaset ya fara wannan harka, inda ya ce; a lokacin baya kusan shekara 40 da suka wuce, suna aiki da wata kyamara wadda ke makale da injinta da ake dorawa a kafada a rike abin daukar hoto a hannu, tana da wani kaset na bidiyo da ake kira ‘Betamad’.
A wancan zamanin, idan muka kammala shirin fim; yawo muke gida-gida, musamman ga wadanda muka san cewa; suna da abin kallo a gidajensu, sai mu rika hada su da Allah su karbi kaset din su je su kalla. Haka mu ka yi ta wahala, har Allah ya kawo mu wannan lokaci da muke yanzu.
Malam ya ci gaba da cewa, a wancan lokacin daga cikin jaruman da ake amfani da su wajen shirya fina-finai, akwai mata masu zaman kansu, haka za ka tafi ka jira su gama abin da suke yi; sannan ka tawo da su wajen da ake shirya fim su yi maka aiki ka biya su, ba kamar yanzu da matasa maza da mata masu mutunci, wadanda ke neman halaliyarsu; suka cika masana’antar ba.
A zamanin baya, duk da cewa fina-finan nanaye sun fi karbuwa a wajen mutane, amma haka muke kokartawa wajen ganin an shigar da wata koyarwa ta addinin musulinci ko kuma wani abu mai amfani da zai amfanar da al’umma ta wani bangare, amma yanzu duk an daina wannan, masu shirya fina-finai na amfani da labarai masu tsafta da amfanarwa, ba tare da da sanya wakoki ko makamantansu a ciki ba, in ji Malam.
“Dalili kuwa shi ne, yanzu ‘ya’yan mutunci da arziki su ne ke yin harkar, sannan kuma su ne suke samun arzikin duniya da na lahira, akwai lokacin da har mata masu zaman kansu din, sai da muka daina samun su idan zamu yi fim, amma yanzu wannan duk ya zama tarihi”, in ji shi.
Game da tambayar da aka yi masa a kan yadda mutane ke kallon sa, duba da cewa; shi malami ne na addinin musulinci, kuma jarumi a Masana’antar Kannywood cewa ya yi, mutane na yi masa kallon wani Waliyyi a cikinsu, duba da yadda yake isar da sako ko warware wasu matsaloli na musulunci da suka shige wa al’umma duhu ta hanyar fim.
Dangane da yadda yake kallon tarbiyar jaruman Kannywood na yanzu maza da mata, Malam ya sake jaddada maganarsa ta cewa; mutanen kirki ne matuka, sannan akwai wasu maganganu da wasu jahilai wadanda ake yi wa kallon malamai suke yi dangane da jaruman wannan masana’anta ta Kannywood, domin idan har wani zai yanke hukunci a kan tarbiyar jaruman Kannywood, to ba zai wuce mu da muke tare da su ba.
Sannan kuma, duk duniya babu wani jarumin fim mutumin kirki irin dan Masana’antar Kannywood, domin kuwa shi kadai ne yake yin fina-finansa da sauran al’amuran rayuwa a gaban jama’a kowa yana gani, ba tare da ya saka wani hijabi ba, sannan dan Kannywood; ba ya ashariya, ba a hada jiki tsakanin mace da namij, ballantana har ta kai ga sumbata kamar yadda muke gani ana yi a wasu masana’antun shirya fina-finai a sauran sassan duniya.
Daga karshe, ya bayyana cewa; dukkannin wani malami da ma wanda ba malami ba, ya sani duk lokacin da ka bayyana wani abu marar kyawu da wani ya yi a boye ko da yana yi, amma sai ya boye yayin da zai aikata wannan abu, to ka sani Manzon Allah SAW ya ce, ba za ka mutu ba sai ka aikata wannan abu da ka ce yana yi, ko da kuwa yana yi din.