HALIMA KASSIM, hazika ce kuma jajirtacciya mai neman na kanta, ta yi jan hankali ga mata kan su yi biyayya ga mazajensu, su nemi halal, sannan su tsaya wuri guda domin kare mutuncinsu da na iyaye kai har ma da na ‘ya’yan da za su haifa. Haka nan ta shawarce su da su kiyaye yawace-yawace da yawan shige-shige marasa amfani.
Halima ta yi wannan jan hankali ne a tattaunawarsu da wakiliyarmu BILKISU TIJJANI KASSIM. Ga dai yadda ta kasance a tsakaninsu:
- Ziyarar Babbar jami’ar Lithuania A Taiwan Shirme Ne
- Ya Kamata A Bar Sinawa Su Yanke Shawara Kan Al’amuran Kasar Sin
Da fari za mu so sanin cikekken sunanki da tarihinki?
Assalamu alaikum warahmatullah. Sunana Halima Kassim, an haife ni a Karamar Hukumar Hadejia Jihar Jigawa. Na yi makarantar firamare a ‘Abdulkadir Special Primary School Hadejia,’ daga nan kuma bayan na gama na tafi Women Teachers College Malammadori, na yi J S S 1,2,3 daga nan na tafi Science Secondary School Jahun na yi S S S 1,2,3.na gama karatuna na secondary.
Shin Hajiya Halima matar aure ce ko kuwa?
Eh to a yanzu dai ba ni da aure bayan na gama sikandire na yi aure ina tare da mijina cikin jin dadi da kwanciyar hankali ya amsa kiran Ubangijinsa wato Allah ya yi masa rasuwa sakamako hatsarin mota an tura shi aiki a hanyarsa ta tafiya.
Shin kun haihu da shi kafin ya rasu ko kuma baku haihu ba?
Eh Allah ya azirta mu da da daya.
Bayan rasuwarsa ba ki sake wani auren ba?
Bayan na gama takaba sai na koma karatu na yi Diploma a Enbironment Menegment, sannan kuma da na samu kamar shekaru uku a tsakani na sake komawa makaranta na yi National Diploma For History yanzu kuma ina H .N.D. na kusa gamawa.
To Hajiya Halima idan kin gama HND za ki ci gaba ne da karatu ko kuma za ki yi aure?
Eh, duk wanda ya samu zan yi in sha Allahu in aure ne muna fatan Allah ya kawo miji nigari.
Hajiya Halima, duk karatun nan da kike yi kina aiki ne ko kuma karatun ne kike ta yi?
Eh to da lokacin ina gidan mijina na samu aiki ina dan yi a Local Gobernment, to tun da Allah yai masa rasuwa na dawo gidammu kara tun dai nake yi sai dai kuma ina taba kasuwanci haka.
Me kasuwanci naki ya kunsa?
Ina sayar da kamar akwai keken dinki da turaren wuta takalma da kayayyaki haka.
Mene ne ya ja hankalin ki kika fada kasuwanci, bayan ga karatu da kike yi?
To neman kudi ai ya zama dole a wannan rayuwar tamu ba sai ka je kana karamar murya kana ruko ba idan kana dan kasuwancin ka za ka rufa wa kanka asiri har ka taimaki wani ma, sannan za ka iya daukar dawainiyar kanka ba za ka nemi kudi a hannunka ka rasa ba, sannan a wajen karatumma za ka samu ciniki sosai to kin ga ka hada abu biyu kenan za ka ci riba biyu.
A zamanki na aure shin kin taba fuskatar wani kalubale kin san rayuwar zaman aure sai hakuri kafin maigida ya rasu?
Eh to ai ba za ka ce komai ba ita dama rayuwa zo mu zauna zo mu saba ce amma dai ni tsakani na da shi babu wani abu da ya taba shiga tsakanina da shi wanda za a ce wai gashi har an shiga tsakaninmu ko kuma wai gida su ji zama muke na nutsu da kwanciyar hankali saboda mutum ne mai kirki da gaskiya da rikon amana babu macen da za ta ce ta same shi a matsayin miji baji dadin zama da shi ba fatana shi ne Allah ya jikan sa da rahma.
To a harkar kasuwanci ki fa ba ki taba samun wani kalubale ba?
Kana kasuwanci ai ba za ka ce baka samu kalubale ba saboda akwai harkar bashi wani zai dau kayanka kafin ya ba ka kudin sai ya wahalar da kai, wani kuma sai ranka ya baci wani ba zai baka kudin ba haka zaka hakura ka barshi, dama haka kasuwanci ya kunsa akwai riba akwai kuma rashin riba sannan akwai faduwa akwai asara sai na ce ni kam Alhamdulillah.
Zuwa yanzu wace irin nasara kika samu a kasuwancinki?
To Alhamdulillah, gaskiya na samu nasarori dama gaskiya ina iya daukar kaina da har ma na taimakawa wani to kinga sai dai na ce Alhamdulillah nasarori na same su da yawa ba zan ma iya kirga su ba gaskiya sai godiya.
Wanne irin addu,a ne idan akayi miki kike jin dadi?
Addu’a duk addu’a ce, kuma duk addu’ar da aka yi maka za ka ji dadi mana har ma a ce Allah yai maka albarka da zuri’a baki daya.
Ada can kafin yanzu mene ne burinki?
A gaskiya ina da burin zama likita na yi ta kokarin hakan amma kin san kana naka Allah yana nasa kuma na Allah shi ne daidai Allah ya sa haka shi ya fi zama alkhairi.
Ga karatu ga kasuwanci ga kuma kula da danki da kika ce an bar miki, ta ya ya kike gudanar da hutunki?
Kasuwanci ai baya hana hutu, sannan kuma karatu ma shi ma idan an yi hutu zan samu na huta, daya kuma ba zai hana ni hutu ba.
Wane irin kwarin kwiwa kike samu a wajen iyaye a kan harkar karatunki da kuma kasuwanci ki?
Alhamdulillah ina samun kwarin kwiwa sosai a wajen iyaye tun suna da rai shi ya sa bayan sun rasu ma ban gajiya ba daga kasuwanci har karatu.
Kawaye fa?
To ni dai gaskiya bani da wata takamaimiyar kawa saboda mu gidammu ba,a fita daga makaranta sai gida sannan mu a tsarin gidammu mun saba da kulle, saboda mu gidammu ko aikin ka aka yi babammu yana kofar gida zai tambaye ka ina za ka idan ka ce aikenka aka yi zai ce ka koma gida a aiki namiji to shi ya sa to shi ya sa ma za ki ga bamu da kawaye.
A karshe wacce irin shawara za ki ba ‘yan ‘uwanki mata?
Shawarar da zan ba wa ‘yan uwana mata duk inda ‘ya mace take ta tsare kanta, sannan kuma ta kiyaye duk wani abubuwa da zai jawo mata matsala a rayuwar ta, ta ji tsoron Allah kuma ta kare kanta da mutunci ta da mutuncin iyayenta ta yi wa kanta mutunci ta bar yawaceyawace da shige-shige, sannan kuma mutum ya tsaya a waje daya ya kama sana’a kar ka ce za ka dogara da wani saboda dogaro da wani ba abu ne tabbatacce ba saboda Allah kadai ne za ka dogara da shi mutum idan ka dogara da wata ran akwai gajiyawa.
Wannan ita ce shawarar da zan ba wa ‘yan’uwana mata, sannan kuma a yi zaman aure a bi miji sau da kafa saboda aljannarki tana karkashi kafar mijinki .