Shugaban mulkin Sojin Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani, ya ce za a yi tafiya da kowa a tattaunawar, wadda zata tsara abubuwan da gwamnati za ta fi bai wa muhimmanci, sannan kuma za ta tsara jadawalin sauyin mulkin.
Jamhuriyar Nijar za ta gudanar da wani taron kasa, domin shata jadawalin tsarin komawa kan tafarkin siyasa, wanda aka dade ana jira, bayan juyin mulkin sojan watan Yulin 2023, wanda ya kifar da gwamnatin zababen Shugaba Mohaammad Bazoum.
- Tawagar Jami’an Jihar Guangxi Ta Sin Ta Ziyarci Kasar Niger
- Dogaro Da Kasashen Yamma Ba Zai Tabbatar Da Tsaro A Philippines Ba
Shugaban mulkin sojin Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani, ya ce za a yi tafiya da kowa a tattaunawar, wadda za ta tsara abubuwan da gwamnati za ta fi bai wa muhimmanci, sannan kuma za ta tsara jadawalin sauyin mulkin.
Wakilin Muryar Amurka a Abuja, Timothy Obiezu ya ruwaito daga Abuja Babban Birnin Tarayyar Nijeriya cewa kodinetan shirye-shiryen sashen Afirka na kungiyar Yiaga Africa Malam Ibrahim Faruk, ya ce wannan taron, wata kyakkyawar hanya ce aka dauka, cikin harshen Tturanci, ya kada baki ya ce “Wannan na nuna alamar farkon jadawalin komawa ga tsarin gwamnatin da ake zaba a dimokaradiyyance a Jamhuriyar ta Nijar.
Ina ganin abin da ya sa hakan ke da muhimmanci, shi ne tasirin kwanciyar hankali a dimokaradiyyance na da wasu hanyoyin yaduwa a Afurka Ta Yamma. Mun ga yadda idan aka yi juyin mulki, ko yinkurin yi, a wasu daga cikin wadannan kasashen, al’amarin kan girgiza yankin. To amma baya ga komawa kan turbar dimokaradiyya kawai, dole al’amarin ya zo da alkawarin kawo irin ci gaban da ke tattare da tsarin dimokaradiyya.”