Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa wasu ‘yan majalisar dokoki na jam’iyyar NNPP za su sauya sheka zuwa APC nan ba da daɗewa ba.
Ganduje ya yi wannan furuci ne a wani taron APC da aka gudanar a Kano ranar Lahadi, yayin da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya raba motoci da babura ga mambobin jam’iyyar. Ya ce NNPP jam’iyya ce da ke gab da rugujewa, don haka manyan jiga-jigan ta da ‘yan majalisa za su tsere zuwa APC.
A taron da aka gudanar a Meena Event Centre, Ganduje ya jaddada cewa APC na ci gaba da karɓar sabbin mambobi daga NNPP. Taron ya samu halartar manyan jiga-jigan jam’iyyar APC a Kano, ciki har da Shugaban APC na jihar, Abdullahi Abbas, da ɗan majalisa Alhassan Ado Doguwa, wanda ya nuna ƙwarin gwuiwa kan nasarar APC a zaɓen 2027.
Sanata Barau, wanda ya shirya taron, ya bayyana cewa rabon motocin da babura wani ɓangare ne na shirin tallafawa al’umma. Ya ce za a ci gaba da ba da goyon baya ga matasa, da ɗalibai, da manoma da ‘yan kasuwa a Kano.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp