Assalamu alaikum, barka da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirin namu na GIRKI ADON MATA.
Yadda Uwargida Za ta Hada Sakwarar Dankalin Turawa: Abubuwan da ya kamata Uwargida ta tanada Dankalin Turawa,Turmi da tabarya.
- Yadda ‘Yan Bindiga Suka Hallaka Ma’aikata Hudu Da ‘Yansanda Biyu A Kamfanin Sarrafa Tasa
- Masarautar Mubi Da Kyakkyawan Shugabancin Sarki Alhaji Abubakar Isa Ahmadu
Da farko za ki fere dankalin kamar yadda a ke fere shi sannan ki yayyanka shi kamar gida biyu zuwa uku ki wanke shi ki sa a tukunya ki dan sa masa ruwa sai ki dora shi a wuta ya yi kamar minti 10 zuwa 15, idan ya dahu sai ki sauke shi ki zuba shi a cikin turmi ki daka shi kamar de yadda za ki yi sakwarar doya ya daku sosai ya yi laushi shikenan za ki iya kulla shi a leda ko kuma ki barshi haka ki zuba.
Za ki iya cinshi da miya jajjage .
Ki samu tattasanki da tumatur idan kina so za ki iya sa dan taruhu sai ki jajjaga su gaba daya ki sa su a tukunya ki tafasa ki soya ki yayyanka albasarki kanana mai dan yawa, ki zuba ki sa magi gishiri kuri da dai sauransu kin san yadda za ki hada miyar jajjagenki ta yi dadi za ki iya sa mata nama. jajjagenki ta yi dadi za ki iya samata nama na (chicken flower), wato soyayyar kazar da ake soyata da fulawa.
Abubuwan da za ki tanada wajen soya kazar da ake soyawa da fulawa sun hada da: Kaza, fulawa, kwai, mai, magi, gishiri, kori da kuma albasa.
Da farko, za ki tafasa kazarki ki sa mata albasa da gishiri da magi, saboda ta dan yi dadi. Idan ta tafasa sai ki sauke ta ki tsame ta a ruwan, idan kin so za ki fara tafasa kazar kafin ki yi miyar jajjagen, saboda ki mata dan ruwan kazar, sannan ki dakko fulawarki ki zuba a wani roba, sai ki sa mata magi da gishiri da kori ki gauraya su.
Sannan sai ki fasa kwai a wata roba ki sa masa albasa saboda karni, kina dakko wannan kazar da kika tafasa kina sawa a cikin kwan kina tsameta, sai ki sa a cikin fulawar kina juyawa kina ajiyewa a gefe har sai kin ga masu gaba daya zakar, sannan sai ki kunna wuta ki dora mai ya yi zafi kisa masa albasa kina soyawa. Idan ya soyu, za ki ga ya yi kaman kalan kasa-kasa, haka za ki yi har ki gama.
Idan kika zuba sakwarar sai ki sa miyar jajjagen a gefe ki jera naman a gefe.
A ci dadi lafiya.