Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), ta sanar da naɗin Dakta Mustapha Muhammad Ali, a matsayin sabon Sakataren Hukumar.
Sanarwar naɗin na ƙunshe ne a cikin wata takarda da shugaban sashin hulɗa da Jama’a na hukumar, Muhammad Ahmad Musa, ya fitar bayan amincewar kwamitin gudanarwa na NAHCON a taron da aka gudanar na ranar 26 ga Fabrairun 2025, bisa tanadin sashi na 8 na dokar da ta kafa NAHCON ta 2006.
- NAHCON Ta Tsawaita Wa’adin Biyan Kuɗin Kujerar Aikin Hajjin 2025 zuwa 10 ga Fabrairu
- Hajjin 2025: Kamfanin Saudiyya Ya Amince Da Kwangilar Aiki Da NAHCON Bayan Sabunta Yarjejeniya
Dakta Mustapha Muhammad Ali, wanda ƙwararre ne wajen tabbatar da gudanarwa da kuma aiwatar da manufofin inganta aikin Hajji a Nijeriya, zai yi aiki a matsayin Sakatare na tsawon shekaru huɗu a matakin farko.
Kazalika gogaggen ma’aikaci ne kuma tsohon babban Sakataren hukumar Jin daɗin Alhazai ta Jihar Borno, kana yana da ƙwarewa mai yawa da zai kawo wa hukumar ci gaba a ayyukanta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp