Janar Mai ritaya, tsohon Darakta Janar na NYSC, ya kuɓuta bayan kwana 22 a hannun ‘yan bindiga. Wata majiya ta tabbatar da cewa an sake shi a daren Juma’a, kuma yana karɓar kulawar likita a wani asibitin da ba a bayyana ba saboda dalilan tsaro.
Tsiga ya faɗa hannun ‘yan bindiga ne a ranar 6 ga Fabrairu, 2025, a gidansa da ke ƙauyen Tsiga a ƙaramar hukumar Bakori ta jihar Katsina. Lokacin harin, mutum biyu sun jikkata, yayin da ɗaya daga cikin ‘yan bindigar ya rasa ransa sakamakon harbin da wani daga cikin mutanensa ya yi.
- Masu Garkuwa Sun Nemi Fansar Miliyan 250 Kafin Su Saki Tsohon Shugaban NYSC, Janar Tsiga
- Ƴan Bindiga Sun Kai Hari A Katsina, Sun Sace Tsohon Daraktan NYSC, Janar Tsiga
Har yanzu jami’an gwamnati da hukumomin tsaro, ciki har da rundunar ‘yansandan Katsina, ba su yi tsokaci kan yadda aka sako shi ba. Ana dai hasashen an biya kudin fansa ko an yi wata yarjejeniya domin kuɓutar da shi.
Tsiga ya shiga hannun masu garkuwa ne bayan da miyagun suka mamaye gidansa da makamai. Rahotanni sun bayyana cewa sun kakkarya ƙofofi, lamarin da ya sa tsohon janar ɗin ya fito don fuskantar su, amma suka yi awon gaba da shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp