Shugaban ƙasar Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ce ba zai yi shawara da Rasha kan tsagaita wuta ba, sai dai idan ta daina kai wa ƙasarsa hare-hare.
“Ukraine tana yaƙi ne don kare kanta da kuma dawo da zaman lafiya. Muna son yaƙin ya ƙare, amma har yanzu Rasha na ci gaba da yi mana luguden wuta,” in ji Zelensky.
- An Fara Haska Fim Din Sin A Sinimomin Najeriya Da Ghana Da Laberiya
- Majalisar CPPCC Za Ta Gudanar Da Taron Shekara-shekara Daga Ranar 4 Zuwa Ta 10 Ga Maris
Ya bayyana cewa cikin mako biyu da suka gabata, Rasha ta kai hare-haren jiragen yaƙi marasa matuƙa guda 1,050, ta jefa bama-bamai kusan 1,300, tare da harba makamai masu linzami sama da 20 domin lalata birane da kashe mutane a Ukraine.
“Idan ana son tattaunawa da mu, to dole a fara da dakatar da hare-haren da ake yi wa al’ummarmu,” in ji shi.
Ya kuma ƙara da cewa dole ƙasashen duniya su haɗa kai idan ana so a hana Rasha ci gaba da kai hare-haren.
A cewar ‘yansandan Ukraine, hare-haren Rasha sun raunata mutane a yankin Donetsk, sannan a ƙaramar hukumar Kherson, mutum biyar sun mutu, yayin da 13 suka jikkata, ciki har da ‘yansanda da suka je ɗauko gawar wani mutum.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp