Shugabar Gidauniyar Yaki da Shayeshayen Miyagun Kwayoyi ta Kasa (YADAF), Hajiya Fatima Bature ta bayyana cewa yawaitar matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi da ke kara ta’azzara a tsakanin matasan yana karuwa ne sakamakon kyamatar su da ake yi.
Shugabar YADAF ta bayyana haka a lokacin da take bayyana sabbin tsaretsaren gidauniyar wanda zuwa yanzu ake kan aiwatar da su.
- Mata A Daina Yawace-yawace Da Shige-shige Mara Amfani -Halima Kassim
- Wike Ga Atiku : Kar Ka Zarge Ni In Ka Fadi A Zabe
Hajiya Fatima ya ce a lokuta dabandaban bisa bincike da tattaunawar da Gidauniyar YADAF ta gudanar tare da sauraron bayanan wasu masu fama da irin wannan matsala, akwai bukatar jama’a da sauran kungiyoyi su sake dabara ta yadda za a daina kyamatar masu wannan dabi’ar, a ci gaba da jansu a jika tare da sauraron bayanansu, ta haka ne kawai za a iya fahimtar hakikanin matsalolin da ke haifar da ta’azzarar annobar.
Ta ci gaba da cewa “Sakamakon binciken da muka gudanar ya tabbatar mana da cewa da yawa daga cikin masu matsalar shaye-shaye sun tsinci kansu a wannan hali ne sakamakon rikon sakainar kashi da wasu iyayen ke yi wa rayuwar yaransu, wasu kuma kuncin rayuwa, wasu rabuwar iyali, wasu munanan abokai da sauransu.
“Saboda haka ba za a fahimci haka ba sai an daina kyamatar su, an ja masu irin wannan matsala ajiki, sannan za su saki jiki su yi bayanin abin da ya kaisu ga fadawa cikin matsalar.”
A karshe Hajiya Fatima ta bukaci malaman Jihar Kano dama kasa baki daya da su yi kokarin shigar da wannan gangami cikin hudubobinsu, domin jama’a a karkara da sauran garuruwan da ke nesa da na kusa su fahimci kyakkawar manufar wannan Gidauniya ta YADAF.
Ta nemi goyon bayan iyayen kasa da malamai a kan lallai su ci gaba aikin da suke yi na wayar da kan al’umma domin kauce wa afkawa cikin wannan ta’ada.