Wata kungiya mai rajin goyon bayan Asiwaju Tinubu a shiyyar Kudu Maso Yamma wato (SWAGA 6), a ranar Asabar ta misalta jigon APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin mutumin da ya fi dacewa da cancantar zama Shugaban Kasa a duk cikin ‘yan takarar da suke neman tikitin a karkashin jam’iyyar mai mulki.
A wani taron manema labarai da kungiyar SWAGA 6 ta yi, daga bisani kuma suka yi jerin gwano a kan titinan Maitama, Wuse 2 da wasu sassan Abuja domin nuna goyon baya ga takarar Tinubu.
Sakataren kungiyar, SWAGA 6, Comrade Babajide Akinbohun, wanda ya yi magana da ‘yan jarida ya nuna cewa Tinubu wani haziki ne da baima bukatar dogon ta’aliki lura da daukakarsa da ficensa a siyasa.
Akinbohun ya ke: “Bisa gabatowar babban zaben cikin gida na jam’iyyar APC mun duba ba mu samu wani da ya fi dacewa da gadar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ba kamar Tinubu. Shi ‘Asiwaju Bola Ahmed Tinubu’ shi ya fi cancanta da dacewar zama shugaban kasa kuma shine zabin mafi rinjaye na al’ummar Nijeriya.
“Asiwaju Bola Tinubu haziki ne, fitacce ne, Farfesa ne a fagen siyasa da bai bukatar sai mun zauna muna gabatar da shi, domin ya yi fice a fagen siyasa, Bada gudunmawa wajen hada kan kasa da ‘yan kasa, tabbatar da zaman lafiya da hadin kai.
“Duk cikar masu bidar tikitin Shugaban Kasa a jam’iyyar mu ta APC babu wanda ya kusan kamo nagartar Tinubu.”
A bisa hakan ne kungiyar suka nemi daliget da al’ummar kasar nan da su cigaba da mara wa Tinubu baya domin ya samu nasarar dalewa karagar mulki.