Kwamitin Majalisar Dattawa kan Ladabtarwa, hakkoki da ƙararraki, a ranar Alhamis, ya bada shawarar dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan na tsawon watanni shida.
Shugaban kwamitin, Sanata Neda Imasuen, ya gabatar da rahoton a zaman majalisa, yana mai cewa Sanata Natasha ta ƙi bayyana gaban kwamitin don kare kanta kan zarge-zargen da ake mata.
- Ramadan: Gwamnatin Sakkwato Ta Rage Wa Ma’aikata Lokacin Aiki
- Kwamitin Majalisa Ya Yi Watsi Da Ƙorafin Da Natasha Ta Shigar A Kan Akpabio
Yanzu haka ‘yan majalisar na ci gaba da tattaunawa kan rahoton kafin yanke hukunci na ƙarshe.
Tun farko dai majalisar ta kai Sanata Natasha gaban kwamitin bayan taƙaddama da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, kan batun zaman kujeru a zauren majalisa.
Daga baya, Sanata Natasha ta zargi Akpabio da cin zarafin jima’i da kuma yin amfani da muƙaminsa ba bisa ƙa’ida ba, lamarin da ya kara tayar da ƙura a majalisar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp