Babban darektan sashen kula da labaran ketare na jaridar The Guadian ta Tanzaniya Benjamin Mgana ya zanta da manemi labarai na kamfanin dillancin labarai na Xinhua inda ya bayyana cewa, “Muna mai da hankali matuka kan manufofin raya tattalin arziki da samun ingantaccen ci gaba da manufofin yiwa sana’o’i kwaskwarima da harkokin diplomasiyya, saboda wadannan abubuwa ba kasar Sin kadai suka shafa ba, za su kawo tasiri mai zurfi ga kasashen Afirka har ma da duk fadin duniya baki daya.”
Mgana ya ce, demokuradiyyar dake shafar kowa da kowa ta Sin na mai da hankali kan wakiltar jama’a da tattauna abubuwan dake jawo hankalin jama’a a kullum da daidaita harkoki a kan lokaci. Ya ce, “Demokuradiyya irin ta Sin ta bambanta da na kasashen yamma, salon Sin na ba da muhimmanci sosai kan dorewar manufofi da tsai da tsare-tsare masu dogon zango, ta yadda za a tabbatar da daidaita harkoki yadda ya kamata ta la’akari da abubuwa masu ruwa da tsaki”.
A cewarsa, yana fatan tarukan za su ci gaba da gabatar da sako mai yakini a bangaren hadin gwiwar masana’antun Sin da Afirka da samar da dabarun kimiyya da bunkasuwar makamashi masu tsabta da sauransu, wadanda za su goyi bayan aikin inganta masana’antu da zamanantar da al’ummar Afirka. Ya ce, “Ra’ayin bunkasa sabon karfin samar da hajoji da hidimomi da Sin ta gabatar na mai da hankali matuka kan kirkire-kirkire a bangaren kimiyya da fasaha da samun ingantacciyar bunkasuwa, matakin da ya dace da bukatun nahiyar Afirka matuka. Afirka na fatan zurfafa hadin gwiwarta da Sin a bangaren na’urorin yanar gizo da aikin noma mai amfani da basirar dan Adam da makamashi masu tsabta da sauran bangarori.” (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp