Manufar Saukar da Alƙur’ani:
“فَاعْلَمْ أَنَّ الْمَقْصُودَ بِالْقُرْآنِ دَعْوَةُ الْخَلْقِ إِلَى عِبَادَةِ اللَّهِ وَإِلَى الدُّخُولِ فِي دِينِهِ.”
Fassara:
“Ka sani, manufar saukar da Alƙur’ani ita ce kira ga halittu su bauta wa Allah kuma su shiga cikin addininsa.” Duba Kitãbu at-Tashīlu fi Ulūmi at-Tanzili [1/5]
Sharhi:
Shehun malami al-Imam Ibnu Juzai Allah Ya yi masa rahama, ya bayyana cewa babban dalilin da ya sa Alƙur’ani ya sauka shi ne kira ga bautar Allah da shiga cikin addininsa. Wannan magana tana da tushen ilimi mai zurfi wanda ke da nasaba da tauhidi da shari’a, da hikimar shiriya.
1. Tauhidi a Matsayin Asalin Kiran Alƙur’ani: Manufar farko da Alƙur’ani ya zo da ita; ita ce tabbatar da tauhidi, wato bautar Allah Shi kaɗai ba tare da sanya masa abokin tarayyaba. Wannan ita ce mafi girman sako da dukan annabawa suka zo da shi. Allah ya ce: “Kuma babu wani Manzo da Muka aiko a gabaninka face sai Mun yi masa wahayi cewa: Lallai babu abin bautawa da gaskiya sai Ni, to sai ku bauta mini.” Suratul Anbiya aya ta 25. Saboda haka, Alƙur’ani ya sauka ne domin ya tabbatar da cewa halitta ta san cewa akwai Mahalicci guda ɗaya, kuma Shi kaɗai ya cancanci bauta. Wannan kira yana nufin a fitar da mutane daga duhun shirka da jahilci zuwa ga hasken tauhidi da sanin Allah.
2. Shiga Cikin Addinin Allah: Manufar Alƙur’ani ta bautar Allah za ta samu ba sai a cikin addinsa. Don haka sai an shiga cikin addininsa da shari’ar da ya saukar, wato addinin Musulunci. Wannan yana nufin a bi dukan dokokin Allah da shari’o’in da suka zo a cikin Alƙur’ani da Sunnah. Allah Yana cewa: “Lalle addini a wurin Allah shi ne Musulunci.” Suratu Ãli Imrãn aya ta 19. Kuma ko mutum ya yarda da bautar Allah amma bai karɓi Musulunci ba, to Allah ba Zai karɓa masa ba, domin Ya ce:” Duk kuma wanda ya nemi bin wani addini ba Musulunci ba, to har abada ba za a karɓa daga gare shi ba, kuma shi a lahira yana cikin hasararru ” Suratu Ãli Imrãna aya ta 85. Wannan yana nuna cewa manufar Alƙur’ani ita ce shiryar da mutane su shiga cikin Musulunci ta hanyar yin imani da Allah da biyayya ga umarninsa.
3. Alƙur’ani A Matsayin Hujja: Saukar da Alƙur’ani yana ɗauke da cikakken tsarin rayuwa wanda yake jagorantar Musulumi a cikin dukan al’amuransu. Ya ƙunshi dokokin ibada kamar sallah da azumi da zakka da kuma hajji, da sauran su. Kuma ya ƙunshi dokokin mu’amala kamar ciniki da aure da kasuwanci, da sauran su. Hakanan Ya ƙunshi kyawawan ɗabi’u kamar gaskiya da zumunta, da , haƙuri da adalci da roƙon amana da sauran su. Kuma ya ƙunshi hukunce-hukunce da shari’a kamar halas da haram. Wannan yana nuna cewa saukar da Alƙur’ani ba wai kawai don sanin Allah ba ne, har ma don rayuwar duniya da lahira.
4. Manufar Saukar da Alƙur’ani ta Ķunshi dukan Halitta: Saukar da Alƙur’ani haske ne ga duniya baki ɗaya, mutane da aljanu, da ƙwari da dabbobi da halittu baki ɗaya, domin dukansu su san hanyar shiriya. Saboda haka, yana kira ga: da bin Alƙur’ani, kowa ya yi imani da Allah kaɗai ne abin bauta ba tare da an sanya masa kini ba. Mushrika da Ahlul Kitabi, wato Yahudu da Nasara da Maguzawa da kowa da kowa da su kaɗaita Allah da bauta, su shiga addininsa, kuma su bi shiriyarsa a kowane al’amari na rayuwarsu.
A taƙaice, wannan magana ta Ibnu Juzai tana bayani a kan cewa Alƙur’ani ya zo ne domin:
1. Kiran mutane su bauta wa Allah shi kaɗai,
2. Shiriyar da mutane zuwa ga addinin Musulunci,
3. Tabbatar da doka da tsarin rayuwa mai cike da adalci,
4. Fitar da mutane daga duhun jahilci zuwa hasken shiriya, domin samun jin daɗin duniya da lahira.
Wannan shi ne babban abin da Alƙur’ani ya zo da shi, kuma dukkan surori da ayoyinsa suna bayani ne akan waɗannan ginshiƙai.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp