Ibu Juzai al-Kalbi Allah ya yi masa rahama ya ce:
“يُؤْمَرُ الْقَارِئُ بِالِاسْتِعَاذَةِ قَبْلَ الْقِرَاءَةِ”
Fassara:
“Ana umurtar mai karatu da yin isti’aza kafin ya fara karatun Alƙur’ani”
Fashin Baƙi:
Wannan umurni yana da tushen shari’a daga Alƙur’ani da Hadisi, kuma yana da hikima da fa’ida da dama. Allah Ta’ala Ya umurci Musulumi da yin isti’aza kafin karanta Alƙur’ani kamar yadda Ya labarta mana haka a cikin Suratul Nahli a aya ta 98. Inda Ya ce:” To idan za ka karanta Alƙur’ani sai ka nemi tsarin Allah daga Shaiɗan korarre (daga rahamar Allah).” Wannan aya ta tabbatar da neman tsarin Allah kafin a fara karatun Alƙur’ani.
Ma’anar Isti’aza:
Isti’aza na nufin neman tsari da kariya da fake wa a wurin Allah Shi kaɗai ban da waninsa daga sharrin Shaiɗan. Domin ƙarin haske duba Ibnu Jarir; Jãmi’ul Bayãni [1/111], Ibnu Kasir; Tafsirul Kur’anil Azim [1/27], da Ibnul Ƙayyim; Badã’i’ul Fawã’id [2/200].
Yaushe ake Isti‘aza?:
Malamai sun yi saɓani dangane da lokacinda za a yi Isti‘aza, sai dai magana mafi ingani da malamai mafiya yawa suke a kanta shi ne ana yin Isti‘aza ne kafin a fara karatu. Domin ƙarin haske duba Ibnu Ibnu Juzai; Kitãbut Tashīl fi Ulūmil Kitãbi [1/30], da Bagawī; Ma’ãlumut Tanzīli [[5/42] da Ibnu Aɗiyya; al-Muharrul Wajizi [1/58], da Ibnul Jauzi; Zãdul Masīri [1/14].
Hukunci Isti‘aza Kafin Karanta Alƙur’ani:
Malamai mafiya yawa sun tafi a kan mustahabbi ne yin isti‘aza a lokacin karanta Alƙur’ani a wajen salla. Amma sun yi saɓani a wajen karatun salla, an hakaitu Imamu Malik ba ya isti‘aza a sallar farilla amma yana yi a sallar asham, shi sa ake yi a sallar nafila. Amma Imam Abu Hanifa da Imam Asshafi’i suna yi isti‘aza a sallar farilla. Akwai waɗanda suke ganin wajibi ne a yi isti‘aza a salla gaba ɗaya. Domin ƙarin haske duba Kitãbu at-Tashīlu fi Ulūmi at-Tanzil [1/30] da Ibnu Kasir; Tafsirul Kur’anil Azim [1/26] da al-Ƙurɗubi; al-Jãmi’u Li’ahkãmil Ƙur’ãni [1/86]
Hikimar Yin Isti’aza Kafin Karanta Alƙur’ani:
Akwai hikimomi masu tarin yaw na yin isti‘aza kafin karatu. Ga wasu daga cikinsu:
1. Kariya daga tasirin Shaiɗan: Shaiɗan yana hana mutum fahimtar Alƙur’ani kuma yana kuma sanya ruɗani. Yin isti’aza na kare mai karatu daga fitinarsa.
2. Tsaftace zuciya: Isti’aza kafin karanta karanta Alƙur’ani yana ba wa zuciya tsarki da nufin Allah a karatu da samin tsoron Allah, tare da tadabburi.
3. Bin sunnon Annabi (SAW): Domin Annabi (SAW) yana Isti’aza kafin ya fara karatu.
4. Tsaftace Baki: Yin isti‘aza yana tsaftace baki daga abuwan da ta aikata na wargi da yasasshen zance, domin shiga karanta maganar Allah cikin tsarki da tsafta.
Daga: Abu Razina, Nuhu Ubale Paki
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp