Ministar kula da ma’aikata da al’umma ta kasar Sin Wang Xiaoping, ta ce kasar za ta kara albarkatu da kudi domin tallafawa samar da ayyukan yi a bana, a wani yunkuri na gina wani tsarin raya kasa mai samar da ayyukan yi.
Wang Xiaoping ta bayyana haka ne a yau Lahadi, yayin wani taron manema labarai kan yanayin rayuwar jama’a da taro na 3 na Majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14, ya gudanar.
A cewarta, rahoton aikin gwamnati na bana ya tsara tare da kara shirya aiwatar da manufofin raya tattalin arziki da kara zuba kudi wajen bunkasa harkokin da suka shafi jama’a, wanda zai samar da goyon baya mai karfi ga raya tattalin arziki da samar da aikin yi. Ta kara da cewa, bangaren samar da aikin yi na kasar ya fara da kafar dama a bana, kamar yadda alkaluma daga watanni biyun farkon bana suka bayyana.
Har ila yau yayin taron, Lei Haichao, shugaban hukumar kula da lafiya ta kasar Sin ya ce matsakaicin tsawon rayuwa a kasar ya kai shekaru 79 a shekarar 2024, karuwar kaso 0.4 idan aka kwatanta da 2023. Ya ce wannan nasara ta zarce abun da aka yi tsammanin samu a cikin rahoton raya kasa karo na 14 tsakanin 2021-2025, kuma an cimma nasarar kafin lokacin da aka tsara. Haka kuma ya nuna cewa kyakkyawar al’adar gargajiya ta kasar Sin da yanayin rayuwa mai aminci da aiwatar da jerin dabaru kamar na shawarar inganta kiwon lafiya a kasar Sin da bada fifiko ga raya bangaren kiwon lafiya, sun yi tasiri kai tsaye kan ingantuwar lafiyar al’umma. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp