Bayan da ta shafe tsawon rabin shekara tana gudanar da bincike da tattaro shaidu, a jiya Jumma’a kasar Sin ta fitar da sakamakon binciken da ta yi, game da yadda kasar Kanada take nuna wa kayayyakinta wariya, sakamakon da ya nuna cewa, irin matakin da Kanada ta dauka a shekarar da ta gabata, wato kara sanya harajin kwastam kan wasu hajojin da ta shigar daga kasar Sin, ciki har da motoci masu aiki da lantarki, da karafa da kuma sanholo, salo ne na nuna wariya. Don haka, kasar Sin ta mayar da martani bisa doka, inda ta kara sanya harajin kwastam kan wasu hajojin Kanada, al’amarin da ya sa aka fitar da rahoton bincike kan kin yarda da salon wariya, wanda ya zama irinsa na farko a duk fadin duniya.
A watan Agustan shekarar da ta gabata ne, kasar Kanada ta sanar da kara sanya harajin kwastam da kaso dari bisa dari, kan motoci masu aiki da karfin lantarki kirar kasar Sin, wanda ya fara aiki daga watan Oktoban shekara ta 2024, tare da kara harajin kwastam na kaso 25 bisa dari kan hajojin karafa da sanholo da kasar Sin ta samar. Makasudin yin hakan shi ne, hada baki da kasar Amurka, wajen sanyawa motoci masu aiki da karfin lantarki da kayan karafa da sanholo kirar kasar Sin harajin kwastam. Manazarta sun yi nuni da cewa, hajojin kasar Sin ne kadai, ita Kanada ta kara wa harajin kwastam, kuma ba tare da gudanar da cikakken bincike ba. Kana, fitar da irin wannan sanarwa ba tare da wata ingantacciyar hujja ba, salon wariya ne da Kanada ta yi, wanda ya kawo illa ga tsarin cinikayya na kasa da kasa.
Rahotannin sun kuma ruwaito cewa, a matsayinta na gani-kashe-nin Amurka, gwamnatin kasar Kanada ta sha nuna adawa da kasar Sin. Amma ba ta samu abun da take so ba. Tun bayan da sabuwar gwamnatin Amurka ta fara aiki tsawon kwanaki 40 ko fiye, ya zuwa yanzu, sau da dama ta ci zarafin Kanada, inda ta ce Kanada “jiha ce ta 51 a Amurka”, har ma ta yi mata barazana ta hanyar sanya harajin kwastam. Irin wannan abun ya zama gargadi ga wasu kasashe ’yan kalilan, wadanda ke fatan samun “afuwa” daga Amurka, bisa matakin da suka dauka kan kasar Sin.
Kasar Sin ba za ta rura wutar rikici ba, amma ba ta tsoro. Kuma tabbas za ta tsaya ga kiyaye muradun kasa da ikon samar da ci gaba, da kiyaye ka’idojin WTO game da tsarin cudanyar sassan kasa da kasa a fannin kasuwanci. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp