Kasar Sin ta ce za ta ci gaba da karfafawa duniya gwiwa ta hanyar samar da ci gaba mai inganci da kara bude kofa da samar da karin kuzari ga farfado da tattalin arzikin duniya da ma ci gaban duniyar.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ce ta bayyana haka, yayin taron manema labarai na yau Talata.
- Ficewar El-Rufai Daga APC Babban Rashi Ne – Tsohon Hadimin Buhari
- El-Rufai Ya Yi Alƙawarin Haɗa Abokan Hamayya Don Yaƙar APC A Zaɓen 2027
Yayin taron, wani dan jarida ya yi mata tambaya cewa, hasashen habakar tattalin arzikin kasar a bana, da gwamnati ta gabatar cikin rahoton aikinta, ya ja hankalin jama’a daga ciki da wajen kasar. Bisa la’akari da koma bayan tattalin arziki da duniya ke fuskanta, ta yaya Sin za ta bayar da sabon gudunmuwa ga ci gaban duniya?
A amsar da ta bayar, Mao Ning ta ce bude kofa shi ne tushen kuzarin tattalin arzikin Sin kuma alkawari ne da Sin ta yi wa duniya. Ta ce kamar yadda rahoton aikin gwamnatin ya bayyana, ba tare da la’akari da sauyin da duniya za ta gani ba, Sin ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen nacewa ga bude kofa da fadada shi ta yadda zai dace da dokokin cikin gida da na duniya, kuma bisa manufofi da dabarun da kasar ta tsara da kanta.
Ta kara da yin tsokaci kan harajin da Amurka ta sanyawa kayayyakin Sin dake shiga kasar, tana mai nanata cewa, idan Amurka ta dage sai ta illata muradun Sin, to Sin za ta mayar da martani. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp