Mutum shida sun mutu, wasu kuma da dama sun jikkata a wani sabon rikici da ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya a kauyen Farin Dutse, yankin Ara a Jihar Nasarawa.
Rikicin ya yi sanadin ƙonewar gidaje, babura, da wata motar ‘yansanda.
- Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [4]
- An Yi Tattaunawar Kasa Da Kasa Mai Taken “Sin A Lokacin Bazara: More Damarmaki Tare Da Duk Duniya” A Birnin Chicagon Amurka
A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yansandan jihar, SP Nansel Ranham, ya fitar a ranar Talata a Lafiya, ya tabbatar da mutuwar mutane shida.
Mutanen sun haɗa da Simeon Madaki, Ayawu Senior, Sunday Wa’azu, Vincent Sunday, Taimako Senior, da Filibus Jatau Mai’anguwa.
Hakazalika, wasu uku sun jikkata, ciki har da Samaniya Wa’azu, Vincent Ezekiel, da Johnson Maikasuwa, inda aka kai su asibiti domin ba sukulawa.
Domin tabbatar da zaman lafiya, an tura ƙarin jami’an tsar tare da haɗin gwiwar sojoji domin daƙile tashin hankali.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp