Aƙalla mutum 26 ne suka rasa rayukansu sakamakon ɓarkewar cutar sanƙarau a ƙananan hukumomin Aliero, Gwandu, da Jega a Jihar Kebbi.
Kwamishinan Lafiya na jihar, Musa Isma’ila, ya bayyana haka a wani taron manema labarai da aka gudanar a Birnin Kebbi a ranar Talata.
- Manyan Jami’o’in Kasar Sin Sun Fadada Daukar Dalibai A Fannin AI Da Manya Tsare-tsare
- Ficewar El-Rufai Daga APC Babban Rashi Ne – Tsohon Hadimin Buhari
A cewarsa, an samu ƙarin mutum 248 da ake zargin sun kamu da cutar, wanda hakan ke nuna yiwuwar ci gaba da yaɗuwar cutar a yankin.
Gwamnatin jihar ta ware Naira miliyan 30 domin siyan magunguna da sauran kayayyaki don hana yaɗuwar cutar.
Sanƙarau ba wai kisa kawai ta ke yi ba, tana haddasa illa kamar makanta, kurmancewa, farfaɗiya, da wasu cututtuka masu tsanani.
Alamomin cutar sun haɗa da ciwon kai mai tsanani, ciwon wuya, tari, da amai.
Yaɗuwar cutar a Kebbi na iya shafar sauran jihohin da ke maƙwabtaka da ita, musamman Zamfara, Sakkwato, da Neja, inda ake yawan tafiye-tafiye tsakanin jihohin.
Hakan na nuni da buƙatar gaggauta ɗaukar matakan kariya don hana cutar yaɗuwa zuwa sauran yankuna.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp