Kasa da shekaru biyu da mulkin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, wasu jiga-jigan jam’iyyar APC sun fara yakin neman sake zabensa a 2027 a yankin arewa.
Duk da cewa jam’iyyar APC ko shugaban kasa a hukumance ba su kaddamar da yakin neman zaben ba, manyan jiga-jigan jam’iyyar APC da suka hada da shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Ganduje da sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, sun yi kira ga shugaban kasa ya sake tsayawa takara a karo na biyu.
- Me Ya Sa Jama’ar Turai Ke Adawa Da Sayen Kayayyaki Kirar Amurka?
- Kasar Sin Ce Ke Kan Gaba A Matsayin Kasar Da Ta Fi Samun Jari Daga Ketare
A kwanakin baya, Ganduje, yayin da yake karbar bakuncin kungiyoyin magoya bayan jam’iyyar APC a shalkwatan jam’iyyar da ke Abuja, ya bukaci ‘yan siyasar arewa masu rubibin tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027 da su kawar da burinsu har zuwa 2031, domin Tinubu zai kammala wa’adinsa na biyu.
Akume, yayin da yake magana a wani shirin gidan talabijin na TBC, ya kuma shawarci tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata, Atiku Abubakar da sauran ’yan arewa da kada su nemi kujerar takarar shugaban kasa a 2027.
An kuma lura cewa an fara yakin neman zaben shugaban kasa a jihohin Kaduna, Kebbi da Kwara, yayin da aka kuma ga allunan sake zaben shugaban kasa a wurare daban-daban a Abuja.
Wannan lamari ci gaban da haifar da zazzafar martani daga jam’iyyun adawa da manazarta siyasa wadanda suka yi zargin cewa hakan ya saba wa dokar zabe da kundin tsarin mulkin 1999 wanda aka yi wa kwaskwarima.
Masana harkokin shari’a da masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin cewa irin wannan kamfen da ba a kai ba, yana kawo cikas ga dimokuradiyya, da bin doka da oda da kuma tsarin zabe.
A watan da ya gabata ne jam’iyyar APC ta kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa, Tinubu da Gwamna Nasir Idris a Jihar Kebbi as zaben 2027.
Taron wanda aka gudanar a babban filin wasa na garin Birnin Kebbi, ya samu halartar ministan kasafi da tsare-tsare na tattalin arziki, Sanata Atiku Bagudu da Gwamna Nasir Idris da dan majalisar wakilai kuma abokin Tinubu, James Abiodun Faleke da karamin ministan ilimi, Yusuf Tanko Sununu da sauran shugabannin APC.
Bayan taron na Kebbi, shugabannin jam’iyyar APC, da suka hada da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau I. Jibrin da sakataren jam’iyyar na kasa, Sanata Ajibola Basiru da ministan noma, Abubakar Kyari da wasu da dama sun lalubo yadda Tinubu zai sake tsayawa takara a yayin wani shirin bunkasa noma da jarin Dan’adam wanda Sanata Saliu Mustapha ya shirya a Ilorin na Jihar Kwara.
Makonnin da suka gabata, masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a Jihar Kaduna sun amince tare da gamsuwa ga Shugaba Tinubu da Gwamna Uba Sani, “Saboda jagorancinsu da manufofin da suka dace da jama’a.”
A wata sanarwa da ya fitar, sakataren jam’iyyar a jihar, Yahaya Baba Pate, ya ce masu ruwa da tsaki sun ba da goyon baya ne a taron da aka gudanar a ofishin kula da Jihar Kaduna da ke Abuja. Wannan ya biyo bayan goyon bayan shugabannin biyu na kara yin wa’adin mulki a karo na da daukacin kansiloli 255 na jihar suka amince da shi.
A karshen mako, a lokacin biki da Ganduje da Sanata Barau Jibrin suka tsara, wasu daga cikin kungiyoyin masu goyon bayan Atiku Abubakar, daga jihohi 19 na arewa, yayin da suke sanar da sauya shekarsu zuwa APC sun yi alkawarin aiki don ci gaban gwamnatin Tinubu a 2027.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp