Ofishin kwamitin kolin JKS da na majalisar gudanarwar kasar Sin, sun sanar da kaddamar da sabon shiri game da tsare-tsaren musamman na bunkasa sayayya a kasar Sin, a gabar da kasar wadda ita ce ta biyu a karfin tattalin arziki a duniya ke kara karkata ga mayar da kasuwannin gida ginshiki, kuma babban karfi na ingiza ci gaban tattalin arzikinta.
Shirin wanda ofisoshin biyu suka yi hadakar sanar da shi a jiya Lahadi, ya kunshi dabarun bunkasa sayayya, da ingiza bukatun cikin gida a dukkanin sassa, da fadada karfin sayayya ta hanyar kara yawan kudaden shiga, da rage nauyin da al’umma ke fuskanta ta fuskar bukatun kudi.
Kazalika, shirin na fatan ingiza karin bukatu ta hanyar samar da ingantattun hidimomin gabatar da hajoji, da kara kyautata muhallin sayayya ta hanyar karfafa gwiwar al’umma don yin sayayya, da magance kalubale dake yiwa al’umma tarnaki wajen sayayya.
Bugu da kari, shirin wanda aka tsara zuwa manyan sassa 8, zai mamaye dukkanin sassa ta hanyar magance mataloli, kamar wadanda ke dakile karuwar kudaden shiga, da masu tarnaki ga ingancin hidimomi, da daga matsayin sayayyar abubuwa da ake mallaka ta manyan tikiti, da kara inganta yanayin muhallin sayayya. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp