Yanzu haka dai Amurkawa sun fara girbar sakamakon matakan gwamnatin kasar mai ci na kara yawan harajin fiton kayayyaki da ake shigarwa kasar daga sassan duniya daban daban, inda matakin ya fara haifar da hauhawar farashi ga iyalai Amurkawa, wadanda suka fara tambayar halin da za su tsinki kai a ciki, idan har sauran sassan da Amurka ta kakabawa karin harajin suka fara aiwatar da nasu matakan na ramuwar gayya yadda ya kamata.
Rahotanni na cewa, tuni wasu Amurkawa suka fara gaggawar sayen kayayyakin bukatun yau da kullum, da nufin adanawa saboda tsaron abun da ka iya faruwa yayin da tasirin martanin kasashen duniya ya fara tsananta a kan kasarsu.
- An Watsa Shirin Bidiyon “Bayanan Magabata Dake Jan Hankalin Xi Jinping” Na Harshen Cambodia
- ‘Yansanda Sun Kama Mutane 157, Sun Ƙwato Bindigu Da Miyagun Ƙwayoyi A Kano
Tun farko dai masana sun sha bayyana wannan karin haraji na gwamnatin Amurka a matsayin matukar kwadayin cin kazamar riba, da yiwa saura matsin lamba domin cin gajiyar kashin kai bisa rashin adalci. Wannan mataki ya haifar da matsin lamba, da gurgunta managarcin tsarin gudanar da ayyukan masana’antu, da rarraba hajojinsu zuwa sassa daban daban na duniya. Baya ga hakan, matakin gwamnatin Amurkan zai jefa ci gaban tattalin arzikin duniya cikin wani mawuyacin yanayi, ciki har da na ita kanta Amurka.
Bugu da kari, illar matakin na Amurka na iya gurgunta salon hada-hadar kudade, da kwadago, da kirkire-kirkire da kasuwannin kasa da kasa ke cin gajiyarsu.
Bisa la’akari da tarihi, mun san cewa Sin da Amurka kasashe ne dake da banbance-banbance ta fuskar ci gaba, da yanayin gudanar masana’antu da karfin tafiyar da su, amma duk da haka ci gaban sassan biyu ya dunkule wuri guda, ta yadda illata sashe daya na iya haifar da koma baya ga dukkanin bangarorin biyu.
Ga misali, yayin da gwamnatin Amurka ke ta yayata manufar karin harajin ramuwar gayya, kamata ya yi mu lura cewa, Amurka na shigo da tarin hajoji da aka kammala sarrafawa, da wadanda ake kara sarrafawa a cikin kasar daga kasar Sin, matakin da ya yi matukar karfafa sashen masana’antun Amurka, ya kuma samarwa Amurkawa masu sayayya damar samun zabi na sayayya, da rahusar farashin abubuwan bukata na rayuwar yau da kullum, da karfafa ikon Amurkawa na sayen hajoji daban daban musamman ma masu matsakaici da karancin kudin shiga.
La’akari da hakan, za mu kara fahimtar cewa, ta hanyar hadin gwiwa tsakanin Sin da Amurka ne kadai manyan kamfanoni, da masana’antun Amurka za su iya kaiwa ga shiga a dama da su a fannin goyayya, da karfafa dunkulewar tattalin arzikinsu, sabanin yadda a yanzu Amurka ke yin matsin lamba, da kakaba haraji na cin zali, wanda zai gurgunta tattalin arzikin dukkanin sassa baki daya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp