A cikin halin da ake ciki yanzu, akasarin masu kiwon Kajin gidan gona, na ci gaba da fuskantar kalubalen da ya hada da rage yawan samun masu sayen Kwai.
Kazalika, suna fuskantar kalubalen dakatar da wasu shirye-shiryen gwamnati, kamar na bai wa daliban makarantar firamare Kwai da sauran shirye-shiryen da gwamnatin ta kirkiro, wadanda suka shafi bangaren bayar da Kwan.
- Bai Wa Shanu Guba: Sojoji Sun Shiga Tsakani Domin Dakile Yunkurin Ramuwar Gayya A Filato
- Ina Dalilin Da Ya Sa Cinikin Shige Da Fice Na Kasar Sin Ke Samun Bunkasuwa Mai Dorewa Ba Tare Da Tangarda Ba?
Kusan za a iya cewa, wadannan matsaloli da masu kiwon Kajin gidan gona ke fuskanta, na kara ta’azzara ne sakamakon ba su kayan ayyukan da za su iya adana Kwan har zuwa wani dogon lokaci, musamman duba da yanayin zafin da ake fuskanta a fadin wannan kasa, ya kara tabarbara al’amuran kiwon baki-daya.
Wadannan matsaloli, sun jawo wa masu kiwon Kajin na gidan gona, sayar da Kwansu cikin farashi mai rahusa, musamman don guje wa tabka asara.
Ya danganta da yadda girman Kwan yake, misali, a babban birnin tarayyar Abuja, a kananan shaguna yanzu, ana sayar da duk kiret daya daga tsakanin Naira 5,000 zuwa Naira 6,500.
Bugu da kari, saboda karancin masu sayen Kwan, musamman sakamakon matsin tattalin arziki da ake fama da shi, ana kara samun masu sayen Kwan don amfani da shi, wanda hakan ya sanya ake ci gaba da samun Kwan da ba a sayar ba.
Misali, a makwanni biyu da suka gabata a garin Jos, an samu matukar raguwar farashin Kwan, inda ake sayar da shi kasa da Naira 3,900 zuwa Naira 4,000.
Sai dai, a wannan makon an dan samu karin farashin, wanda ya kai daga Naira 4,200 zuwa 4,300.
Daya daga cikin irin wadannan masu kiwon Kajin na gidan gona, Muhammad Bello Ibrahim, ya bayyana bacin ransa kan yadda wannan matsala ke ci gaba da faruwa.
“Masu sana’ar kiwon Kajin a yanzu haka, suna ci gaba da fuskantar kalubalen rashin samun masu sayen Kwan,” in ji Bello.
Ya ci gaba da cewa, a baya; a karkashin shirye-shiryen ciyarwa na gwamnati, ana karfafa wa wasu jihohin sayen Kwan da ake bai wa ‘yan makarantar firamere, domin amfanin marasa lafiya da aka kwantar a asibiti da kuma amfanin wadanda ake tsare da su a gidan gyaran hali, amma kusan yanzu, shirye-shiryen sun tsaya cak.
Bisa wani bincike da aka gudanar a garin na Jos, duk da raguwar da aka samu na farashin Kwan, ana ci gaba da fuskatar karancin masu saye, wanda kuma hakan ya sa ake samun kwantan Kwan.
Hakan na kuma faruwa ne a yayin da ake ci gaba da fuskantar tsananin zafi, a jihohin kasar ciki har da garin na Jos.
Wata mai kiwon Kajin gidan gona a Jihar Filato, Nanji Gambo-Oke, ta sanar da cewa, kiwon Kajin a jihar, na fuskanta babban kalubale.
A cewar tata, kashi 80 cikin dari na Kwan da ake kyankyashewa a jihar, makwabtan jihar ne ke zuwa saye, ciki har da babban birnin tarayyar Abuja.
Ta kara da cewa, a bangaren gwamnatin jihar kuma tana nuna halin ko in kula dangane da kwantan Kwan da masu kiwon a jihar ke ci gaba da samu.
“Babu wani dauki da masu kiwon Kajin gidan gonar a jihar ke samu daga bangaren gwamnatin jihar, wanda hakan ke ci gaba da jefa su cikin halin tsaka mai wuya”, in ji Nanji.
Sai dai, Shugabar Kungiyar Masu Kiwon Kajin Gidan Gonar, reshen jihar Madam Shinkur Angela Jima, ta sanar da cewa, gwamnatin jihar na nuna goyon baya ga fannin.
Ta kara da cewa, a yanzu haka, gwamnatin na kokarin samar da tsare-tsaren da za ta tallafa wa masu kiwon a jihar.
Bugu da kari, a Jihar Neja ma, masu kiwon Kajin na ci gaba da fuskantar kalubalen rashin samun masu sayen Kwan da kuma rashin samun kayan aiki na zamani, wanda hakan ke jawo lalacewar Kwan nasu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp