Mai koyarwa Hyda Ahmad Ghaddar, mai shekaru 27 da haihuwa, tana horar da matasa kwallon kafa a kungiyarta mai suna ‘Breakthrough Football Academy’, ma’ana makarantar da matasa za su samu damar tsallakawa zuwa kasashen waje cikin sauki kuma ba tare da yaudara ba ko kuma damfara kamar yadda aka bayyana wasu makarantun suna yi wa matasan da suke son tsallakawa nahiyar turai.
Matashiya Hyda, ta fara buga kwallo ne tun tana ‘yar shekara shida da haihuwa tare da ‘yan uwanta a kofar gida a cikin birnin Kano.
- Kwararru Sun Yi Musayar Ra’ayoyi Dangane Da Wayewar Kan Sin Da Afirka
- Yadda Hukuncin Kotun Koli Ya Kara Dagula Rikicin Shugabanci A PDP Da LP
An dai haifi Hyda a Lebanon amma iyayenta sun koma birnin Kano a lokacin da take ‘yar watanni biyu, inda ta shafe shekara 16 a Kano kafin daga baya ta sake komawa kasar Lebanon din bayan kammala karatun jami’a a Jihar Kano.
A kasar tata ta asali wato Lebanon ne Hyda ta tsunduma harkar wasan kwallon kafa gadan-gadan, inda har ta shiga makarantu na samun horo a fannin horar da kwallon kafa a Lebanon da Burtaniya. Sannan ta buga kwallon kafa a Nijeriya da Sifaniya da Burtaniya da kuma Lebanon, amma kuma Hyda ta so yin kwallo kafa a matsayin kwararriyar ‘yar kwallo sai dai a sakamakon rauni da ta samu ya sa sauya tunaninta zuwa mai horar da ‘yan kwallon kafa.
Ta yi digirinta na farko a fannin kimiyyar motsa jiki da kiwon lafiya wato PHE, sannan ta yi digiri na biyu sannan ta yi kwasa-kwasai a fannin kociya har ma ta yi karatun bayar da horo ga masu son zama kociya, sannan tana kuma da lasisi daban-daban kan horar da ‘yan kwallo wanda hakan ne ya kara mata kwarin gwiwa na ganin ta dage wajen cimma burinta na koyarwa.
Hyda ta bude kungiyar kwallon kafa ta ‘Breakthrough Football Academy’ a Kano watanni shida da suka gabata inda take da burin bai wa Kanawa dama su shiga duniyar wasanni inda a hirarta ta sashin Hausa na BBC ta ce ta zama kociya ce saboda tunanin da take da shi na taimakon al’ummar Kano bisa la’akari da irin taimakon da al’ummar Kano suka yi mata itama.
Ta ce “Babban burina shi ne samun wasu daga cikin wadanda nake bai wa horo sun yi fice a duniyar kwallo.” Ta kuma kara da cewa wani karin burin nata shi ne a samu babbar kungiyar wasa ta mata zalla a Kano “Domin a Kano akwai matan da suka iya kwallon kafa amma saboda rashin dama ba a jin su.”
Kungiyar tata mai suna ‘Breakthrough Football Academy’ na gayyato ‘yan wasa kuma “idan sun ga mutum ya yi musu sai su rike shi idan kuma bai dace ba sai su ba shi hakuri. Hyda Ahmad Ghaddar ta yi wasan kwallon kafa inda kuma ta fi taka ‘yar wasan tsakiya sannan ta ce ta samu kwarin gwiwa daga iyalinta tun daga farko kasancewarsu masu son kwallon kafa ne.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp