Jakadan ƙasar China a Nijeriya, Yu Dunhai, ya yi kira ga al’ummar duniya da su haɗa kai don yaƙi da yawan haraji da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ke ƙara wa ƙasashe da dama, yana gargadin cewa wannan mataki na iya janyo koma baya ga tattalin arziƙin duniya tare da illoli masu tsanani musamman ga Afrika.
A lokacin taron manema labarai da ya yi a Abuja ranar Juma’a, jakadan ya jaddada cewa matakan Amurka sun take haƙƙin ƙasashe da dama, sun saɓa dokokin yarjejeniyar kasuwanci ta duniya (WTO), suna kuma kawo matsala ga tsarin ciniki na ƙasa da ƙasa da zai iya haifar da rushewar tsarin tattalin arzikin duniya.
- Trump Ya Dakatar da Harajin Da Sanya Wa Ƙasashen Duniya, Ya Ƙi Cire Wa China
- EFCC Ta Gurfanar Da Ɗan China A Kotu Kan Bayar Da Bayanan Ƙarya
Ya bayyana cewa, “Al’ummar duniya dole ne su haɗa kai su yaƙi wannan zalunci domin kare abubuwan da suka shafi al’umma baki ɗaya. Ya ƙalubalanci amfani da haraji a matsayin abin cin fuska ko tirsasawa daga Amurka da nufin tsayawa kan daidaito da gaskiya da kuma adalci.”
Shugaban Amurka ya ƙara tsananta haraji ga ƙasashe da dama, China tana cikin waɗanda suka fi fuskantar ƙarin haraji mai yawa, da 145% na kayan China da sazu shiga kasuwar Amurka, yayin da Beijing ta mayar da martani da haraji na 125% kan kayan Amurka.
Ƙasashe da dama ciki har da Tarayyar Turai (EU) sun ɗora haraji a kan Amurka, wanda ya sa gwamnatin Trump ta dakatar da aiwatar da sabon tsarin haraji na kwanaki 90 domin buɗe damar tattaunawa.
Jakada Dunhai ya ƙara da cewa wannan tsarin haraji yana keta ƙa’idar tattalin arziƙi da dokokin kasuwanci, da ƙin la’akari da cewa Amurka ta daɗe tana cin riba daga kasuwanci na ƙasa da ƙasa.
“Amfani da haraji a matsayin makami don matsin lamba da son rai yana nuni da tsarin siyasa na rashin haɗin kai da kare tattalin arziƙi da kuma zambar tattalin arziƙi. Wannan ba abu ne na adalci ba ko mai kyau – yana nufin zaman ‘Amurka da tafi kowa’ da kuma ƙaruwar ƙarfin Amurka,” in ji shi.
Jakadan ya kuma yi gargadi cewa ƙasashe masu tasowa za su fi shan wahala daga wannan tsarin haraji, kuma hakan zai fi cutar da ƙasashen Afrika, ciki har da Nijeriya.
Ya bayyana cewa, “Amurka ta ɗauki mataki mara son Rai, na cewa ‘ samun ribar kasuwanci sai an yi zamba’ wanda ya kai ga kai wa ƙasashen Afrika haraji mai yawa, wanda ya saɓa wa ƙa’idojin WTO na bayar da kulawa ta musamman ga ƙasashen masu tasowa.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp