An labarta cewa, jimmilar adadin kudin shiga da manyan kamfanonin kera na’urorin sadarwa na kasar Sin suka samu a shekarar 2021, ya kai sama da kudin Sin yuan triliyan 14.
Mataimakin shugaban hukumar bayanan sadarwa, a ma’aikatar masana’antu da sadarwa ta kasar Sin Shi Huikang, ya yi bayani a dandalin kaddamar da bikin baje kolin na’urorin sadarwa na kasar Sin karo na goma a jiya Talata cewa, a farkon rabin shekarar bana, adadin darajar sana’ar kera na’urorin sadarwa ta kasar Sin ta karu da kaso 10.2 bisa dari, idan aka kwatanta da makamancin lokaci na bara, adadin da ya taka babbar rawa ga ci gaban tattalin arzikin kasar ta Sin.
An lura cewa, a halin yanzu, na’urorin zamani da aka kera ta hanyar amfani da fasahohin kirkire-kirkire suna karuwa cikin sauri a kasar Sin, kana haduwar fasahar sadarwa da tattalin arziki tana kara zurfafu.
Ana iya cewa, fasahar sadarwa tana zamanantar da tattalin arzikin kasar Sin yadda ya kamata.
Ana gudanar da bikin baje kolin na’urorin sadarwa na kasar Sin karo na goma, a birnin Shen Zhen na lardin Guangdong dake kudancin kasar tsakanin ranar 16 zuwa 18 ga wannan wata, bikin da ya samu halartar kamfanoni sama da 1400. (Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa)