Ƴan ta’adda da ake zargin Boko Haram ne sun kashe mutane 10 na yawucin dabbobi da kuma mambobin jami’an tsaron sa kai (CJTF) a garin Kwapre, dake cikin ƙaramar hukuma ta Hong a Jihar Adamawa.
Shugaban ƙaramar hukuma, Hon Usman Wa’aganda, ya tabbatar da wannan lamarin ga LEADERSHIP ta waya a ranar Lahadi a Yola, inda ya bayyana cewa wani mutum da ya samu raunuka daga harin ‘yan ta’addan yana samun kulawar likita a wani asibiti da ba a bayyana sunansa ba.
- Daidaikun Kasashe Za Su Kara Karfi Idan Suka Hada Hannu Tare
- ‘Yansanda Sun Kama Wani Kato Bisa Zargin Cin Zarafin Wata Mata A Adamawa
Wa’aganda ya ce ‘yan ta’addan sun ƙone gidaje da dama da kuma amfanin gona, yana mai cewa wannan harin ba na farko bane, domin garin ya sha hare-hare sau da dama wanda ya haifar da asarar rayuka da dukiyoyi.
Ya nemi hukumomin tsaro su ƙara tura jami’ai a yankin domin taimakawa wajen kare al’umma da kuma tabbatar da tsaro.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp