Aƙalla mutane takwas ne suka rasa rayukansu yayin da wasu uku suka jikkata, sakamakon fashewar bama-bamai a ƙaramar hukumar Gamboru Ngala a Jihar Borno.
Majiyoyi sun bayyana cewa fashewar ta faru ne da misalin ƙarfe 11 na safiyar Litinin, yayin da wasu motoci daga Rann, hedikwatar ƙaramar hukumar Kala-Balge, ke kan hanyarsu zuwa Gamboru Ngala suka taka bama-baman da ake zargin ’yan Boko Haram suka dasa.
- Shin Amurka Na Iya Komawa Kan Kadaminta A Matsayin Cibiyar Masana’antun Duniya?
- Akwai Ƙarin Gishiri A Yawan Masu Sauyin Jam’iyya Zuwa APC – El-Rufai
Fashewar ta auku ne a kusa da ƙauyen Furunduma, kimanin kilomita 11 daga Rann.
Mata da yara na cikin waÉ—anda abin ya rutsa da su.
Wani jami’in rundunar HaÉ—in Gwiwa ta ‘Yan Sa-kai (Civilian Joint Task Force) da ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da cewa mutane takwas ne suka mutu.
Wata majiya kuma ta bayyana cewa adadin mutanen da suka mutu na iya fin haka, duba da yawan mata da yara da lamarin ya rutsa da su.
A lokacin haÉ—a wannan rahoto, hukumomin soji da ‘yansanda ba su fitar da wata sanarwa ba dangane da lamarin ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp