Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), ta dawo da ‘yan Nijeriya 203 da suka maƙale a ƙasar Libya.
Sun iso Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed da ke Legas da misalin ƙarfe 7 na yammacin ranar Litinin a wani jirgin Al Buraq mai lamba 5A-BAC.
- Wang Yi: Neman Sulhu Da Ja Da Baya Riba Ne Ga Masu Son Cin Zali
- Rashin tsaro: Gwamnan AbdulRahman Ya Gana Da Sarakuna Masu Daraja Ta Daya A Jihar Kwara
NEMA ta bayyana hakan a shafinta na X (Twitter) a ranar Talata.
Cikin waɗanda aka dawo da su akwai maza 50, mata 96, yara 29 da kuma jarirai 28.
Dawowar tasu ta samu ne da taimakon Hukumar Kula da Hijira ta Duniya (IOM) ƙarƙashin shirin dawo da ‘yan ci-rani da suka maƙale.
Haka kuma wasu hukumomin gwamnati sun taimaka, ciki har da Hukumar ‘Yan Gudun Hijira ta Ƙasa, Hukumar Shige da Fice, Hukumar Tsaro ta DSS, Hukumar Lafiya ta Tashar Jirgin Sama da Rundunar ‘Yansanda.
Mutane biyu daga cikin waɗanda aka dawo da su na fama da matsananciyar rashin lafiya, kuma an garzaya da su asibitin New Ikeja don a duba lafiyarsu.
Bayan an yi musu rijista da ɗaukar bayanan yatsunsu, an mayar da su cibiyar mazauna ‘yan gudun hijira da ke Igando, a Jihar Legas, inda za su samu taimako don ci gaba da rayuwa.
NEMA ta ce wannan wani ɓangare ne na ƙoƙarinta na tallafa wa ‘yan Nijeriya da ke cikin mawuyacin hali a ƙasashen waje da kuma taimaka musu su farfaɗo da rayuwarsu cikin aminci a gida.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp