Dan takarar shugaban kasa a jamiyyar NNPP Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya sanar da dalilin da ya sa NNPP ba za ta iya cika bukata daya da bangaren magoya bayan tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Malam Ibrahim Shekarau suka bukata ba.
Kwankwaso wanda ya bayyana hakan a hirarsa da kafar yada labarai ta BBC Hausa, ya kuma shelanta cewa, ba bu Rigimar siyasa da ke a tsakanin sa da Shekarau.
Ya ce, Jita-Jitar da ake yadawa cewar akwai rikicin siyasa a tsakaninsa da Shekararu karya ce tsagwaronta.
Kwankwaso a kan martanin da ya mayar na cewa mai yuwa Shekarau ya canza sheka zuwa PDP in har NNPP ba a cika yarjejeniyar da suka cimma ba da Shekaru kafin ya dawo cikin NNPP ba
a cewar Kwankwaso, babu wata jarjejeniyar da ba a cika ta ba in banda ta ‘yan takara kuma mun yi iya kokarin mu don girmama wannan yarjejeniyar.
Ya kara da cewa, akasarin mutanen da Shekarau ya taho da su zuwa cikin NNPP zai yi wuya su samu tikitin tsaya wa takarar domin abin ya zo ne dai dai da lokacin da INEC ba za karbi wani dankara ba.
Sai dai, Kwankwaso ya ce, idan NNPP ta kafa gwamnati magoya bayan Shekarau za a iya nada su a kan mukamai masu tsoka.
Kwankwaso ya ce, wannan ba wata matsala bace a NNPP