Akwai fargabar cewa, nan gaba kadan Nijeriya za ta zama kasa mai jam’iyya daya, amma ba a humance ba, kamar qasar Sin, ta hanyar zagon kasa ko wasu sharuxxan doka da gangan kwatankwacin kasashen Kamaru, Uganda, Equatorial Guinea ko Ruwanda, inda jam’iyyun da ke mulki ke yi wa ‘yan adawa kisan mummuke.
Masu bayyana wannan damuwa, sun kawo dalilai da dama, amma babban abin da ya fi daukar hankali ga dukkanin alamu shi ne, guguwar sauya sheqa zuwa jam’iyya mai mulki (APC), wadda ta durkusar da babbar jam’iyyar adawa ta PDP. Yadda Ake Sauya Sheka, baya ga ‘yan majalisar tarayya daga Jihar Osun zuwa Jihohin Kaduna da Neja da suka sauya sheka a ranar 25 ga watan Afrilu, Gwamna Sheriff Oborevwori na Jihar Delta da wanda ya gabace shi, Ifeanyi Okowa da kuma sauran kaukacin jam’iyyar PDP na Delta, suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC, inda ake rade-radin sauya shekar wasu da dama a fadin qasar. Akwai yiwuwar nan ba da jimawa ba, jihohi biyar daga cikin shida na Kudu-maso-kudu, wadanda su ne tushen PDP tun 1999, su ma za su bar jam’iyyar.
- Atiku Ya Soki Tinubu Kan Ayyana Dokar Ta-ɓaci a Jihar Ribas
- Tinubu Ba Ya Tsoma Baki A Ayyukan EFCC – Olukoyede
Wadanda abin ya shafa, musamman wasu daga ‘yan jam’iyyar PDP da sauran al’umma, suna ganin wannan ba sauya sheka ba ne, illa kawai dai suna kulla yarjejeniya ne da ‘yan siyasa don guje wa shari’a ko tuhume-tuhumen da Hukumar EFCC ke yi musu, ko kuma don cimma wata manufa ta siyasa ta gwamnoni da sauran masu sauya shekar.
Sun zargi Gwamnatin Shugaba Tinubu da hannu wajen haddasa ficewar, saboda burinsa na lashe zaven 2027, domin kuwa tsarinsa na ofis ba zai bar shi ya kai labari ba. Neman Mafaka a ganina, wannan zancen banza ne kawai. Amma duk da cewa, bai yi amfani da wadannan kalamai ba, tsohon Mataimakin Shugaban Qasa Atiku Abubakar, saboda son rai irin nasa, ya bayyana cewa; ya yi amanna tare da tabbatar da cewa, sauya sheka gaskiya ce a siyasar Nijeriya, sannan wadanda suke sauya shekar, na amfani da ‘yancinsu ne da doka ta tabbatar musu.
Shi kansa da ya sha sauya shekar, sannan ya yi takarar shugabancin qasa har sau shida, akwai mamaki idan aka ji ya faxi wani abu mara dadi a kan sauya sheka. Matsalar a cewar Atiku, ba ta sauya sheka ba ce, illa aikin da aka yi cikin shekaru biyu da babu wani banbanci, ba za su bar shugaban qasar ya sake komawa kujerarsa ba.
Sai dai kuma, idan Atiku da sauran ‘yan adawa suka ji tsoro, wanda hakan mai yiwuwa ne, kuma Tinubu ya sake cin zaven 2027, wanda shi ma zai iya yiwuwa, hakan ba zai zama saboda sauya sheka ba ne; domin kuwa tuni Atiku ya share fagen ruguza PDP, don kuwa ya nuna shi ne yake da jam’iyyar, abin da ba a cika fada ba, saboda yana jin dadin qalubalantar Tinubu. *Damar Da Ta Kuvuce
Misali, jigo a jam’iyyar PDP, Sule Lamido a ranar Talata ya bayyana cewa; “Ya kamata shugaban qasa ya yi adalci, ya ceci ‘yan adawa daga murkushewa. Ba ni da tabbacin nawa Lamido zai biya Tinubu, saboda zaluntarsa.Wani abin mamaki shi ne, xaya daga cikin wadanda suka kafa PDP, bai san cewa wasu tsiraru daga cikin wadanda suka kafa tan sun ruguza ta ba, sannan babu wanda zai iya farfado da ita sai wasu daga cikinta.
Mafi kyawun damar da ta samu tun bayan rasa mulki shekaru 10 da suka wuce, shi ne shekarar 2023 lokacin da APC ta tsinci kanta cikin mawuyacin hali. Daidai lokacin Gwamnatin Muhammadu Buhari ta dauki mamayar da PDP ta yi a matsayin tamkar wani kisan kai. Saboda haka, Lamido ya fi kowa sanin cewa, Atiku ya saki hanya.
Mirgina Dutse Wurin Da Babu Gansa-kuka
Bayan ya tsaya takara a jam’iyyar APC ya fadi a zaven 2014, Atiku ya sake sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP a shekarar 2017, ya kuma sake tsayawa takarar fidda gwani a 2019. A wancan lokacin PDP ta fara farfadowa daga mummunan kayen da ta sha a 2015, inda ta rasa jihohi tara daga cikin 22 da kuma kujeru 93 na majalisar dokoki ta kasa.
A tsarin zaven shugaban kasa kuwa, PDP ta sha mummunan kaye, lokacin Atiku baya nan. Sai dai, a hankali an sake gina jam’iyyar musamman da gudunmawar Gwamnan Jihar Ribas na wancan lokacin, Nyesom Wike. Har lokacin da Atiku ya dawo jam’iyyar, ba ta farfado ta koma kamar yadda take a baya ba. Rikicin da jam’iyyar APC ta samu a karkashin shugaba Buhari, da bangaren jam’iyyar kafin zaven 2023, da kuma yanayin da ake ciki a wancan lokacin ya nuna cewa; Nijeriya na cikin mawuyacin hali. Kasar ta gaji da mulkin APC.
Amma Atiku da yake shi Atiku ne, yana jin cewa ya zama dole a tabbatar da hasashen da aka yi a shekarar 1998 na cewa; wata rana zai zama shugaban kasa.Babu shakka, wannan neman shugabanci ya haifar masa da matsala tsakaninsa da Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo a 2003; tsananin son mulkin nasa ne yasa ya fice daga PDP zuwa ACN, daga bisani kuma ya sake komawa APC. A karshe kuma, kishirwar wannan mulki ce tasa shi sake dawowa PDP.
Neman Wanda Za A Xora Wa Laifi
Ya riga ya zama tarihi, PDP ta sha kasa. Jam’iyyar da ta bugi kirji cewa, ita ce babbar jam’iyya a Afirka, wadda za ta yi mulki na tsawon shekara 60, yanzu ta kare mata, ta fada cikin rubibi, ‘ya’yanta sun koma neman mafaka da inda za su samu su huta a duk inda suka samu kansu.Ta yaya za a danganta wannan matsala da Tinubu, bayan Atiku yana nan yana kyallin goshi?
Duk da cewa, na fahimci halin da da ‘yan adawa ke ciki, amma kuma hakan ba yana nuna cewa, a rika dora wa wani laifin da ba nasa ba. Har yanzu akwai sauran shekara biyu, da za a iya yin wani abu. Yunkurin da Peter Obi ya yi na tsawon wata tara a babban zaben da ya gabata da kuma tasirin da jam’iyyar ta LP ta yi ya nuna cewa, masu kada kuri’a a lokacin zabe na da matukar tasiri wajen kawo sauyi. Wannan mai yiwuwa ne. Ba jam’iyyar da ‘yan son rai ke jagoranta ba, wadanda ba su da wani aiki sai shinshine-shinshine.
Kana iya fadan duk abin da kake so a kan Tinubu, amma tuni shi ya samu daukaka a siyasa tsawon shekaru 30 da suka wuce, domin kuwa ya iya tsayuka da kafarsa ba tare da jingina da wani ba, ya kuma kai labari tare barin kyakkyawan tarihi.
Tafi Atiku, Tafi
Idan har PDP na son yin abin arziki a nan gaba, sannan kuma Atiku ya damu da ita, to lallai ne ya gaggauta janye burinsa na sake tsayawa takara. Wannan buri dai, shi ne musabbabin rigingimun da ke faruwa a jam’iyyar; shi yasa ma PDP ta dare gida uku a jajiberin zaben da ya gabata; wannan tasa ya kasa yin wani tasiri tsawon shekaru biyu. Sannan kuma, shi ne dan takarar shugaban qasa na farko a Nijeriya da wadanda suka tsaya a matsayin mataimakansa suka sauya sheqa daga jam’iyyar. Don haka, babu wani dalili na zargin Tinubu ko nuna fushi a kan Okowa, don ya yi amfani da damar da ya samu. PDP za ta iya farfadowa ne kadai, bayan Atiku ya ja da baya, ya bar ta ta shaki iska. Amma idan ba haka ba, za a ci gaba da bata lokaci ne kawai.
Ishiekwene, shi ne Babban Edita kuma Babban Mataimakin Shugaban Kamfanin LEADERSHIP, sannan marubucin littafin ‘Writing for Media and Monetising It’.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp