Jami’ar Tarayya ta garin Gashua (FUGA), ta samu gagarumar nasara a kokarin da take yi na bunkasa fannin aikin noma.
Ta samu wannan nasara ce, biyo bayan sashen bunkasa kimiyyar dabbobi ta Jami’ar ya samu nasarar kaddamar da injin kyankyasar ‘yan Tsaki na zamani.
- Tanzaniya Ta Yi Maraba Da Zuwan Tawagogin Yawon Shakatawa Na Sin
- Har Yanzu Manyan ‘Yan Wasa Suna Son Buga Wasa A Manchester United – Amorim
A cikin sanarwar da shugaban sashen samar da bayanai na Jami’ar, Mallam Asamu Saleh ya fitar ya bayyana cewa; kaddamar da injin kyankyasar, tamkar ya bude wani sabon babi ne ga sashen na bunkasa kimiyyar dabbobi na Jami’ar.
Saleh ya ce, kaddamar da injin kyankyasar, musamman saboda jajircewar ma’aikatan sashen kan wannan aiki, tuni Jami’ar ta fara ganin sakamako mai kyau.
Ya kara da cewa, samar da wannan inji, ya kara nuna irin mayar da hankali da Jami’ar ta yi, wajen habaka fannin aikin noma ta hanyar amfani da kimiyyar zamani da kuma samar wa daliban fannin kimiyyar Jami’ar kayan aikin zamani da za su rika gudanar da ilimin yin gwaje-gwaje da kuma bayar da gudunmawa wajen kara samar da wadataccen abinci a kasar.
Kazalika, wannan nasara ta kuma nuna a zahiri irin kyakkyawan shugabancin Shugabar Jami’ar, Farfesa Maimuna Waziri, duba da irin kokarinta na dora Jami’ar a kan turba mai dorewa, musamman a bangaren samar da fasahar kirkire-kirkire a fannin aikin noma.
Shi kuwa, a nasa martanin, shugaban sashen bunkasa kimiyyar dabbobi na Jami’ar, Dakta Lawan Adamu ya bayyana cewa; an faro aikin samar da injin kyankyasar ‘yan Tsakin ne, a lokacin shugabancin Tsohon Shugaban Jami’ar, Farfesa Andrew Haruna.
Ya sanar da cewa, sai dai ba a fara amfani da injin ba, sai a lokacin shugabancin Shugabar Jami’ar ta yanzu, Farfesa Maimuna Waziri, wadda kuma ta kara mayar da hankali wajen ganin an kammala aikin injin, domin amfanin daliban sashen bunkasa kimiyyar dabbobin, domin su fara gudanar da gwaje-gwaje a kanta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp