Wasu ‘yan’uwa bakwai a cikin iyali daya sun rasu a kauyen Danbaza da ke karamar hukumar Maradun a Jihar Zamfara bayan sun ci dambu da aka hada da tsakin masara da ganye.
Wakilin LEADERSHIP a Gusau, Umar Mohammed ya aiko da rahoton cewa lamarin ya faru ne a ranar Litinin bayan da ‘yan’uwan suka ci dambun a matsayin abincin dare. Wadanda abin ya shafa dai akwai matan aure su biyu da kuma matasa su biyar.
Wani na kusa da ’yan’uwan, Muhammad Kabir ya ce da mutanen suka kammala cin abincin, hudu daga cikin wadanda abin ya shafa sun mutu nan take, yayin da uku kuma aka garzaya da su asibiti.
Majiyar ta ci gaba da cewa mutanen uku da aka kai su asibiti sun mutu su ma daga bisani inda tuni aka yi musu jana’iza. A cewarsa, ana tunanin sun dafa dambun ne tare da guba.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan’sandan, SP Muhammad Shehu, ya ce bai san da faruwar lamarin ba, amma ya yi alkawarin binciko lamarin daga ofishin ‘yan`sanda na karamar hukumar Maradun. Sai dai Shehu bai tuntubi wakilin namu ba har zuwa hada wannan rahoton.